Tinubu: Tattalin arzikin Najeriya na nan Daram
May 29, 2025Shugaba Bola Ahmed Tinubu wanda ya cika shekaru biyu a karagar mulki ya ce sauye sauyen da ya aiwatar wadanda suka jawo mummunan tsadar rayuwa da aka dade ba a gani ba a kasar suna haifar da sakamako mai kyau.
Bayan da ya hau karagar mulki a watan Mayun 2023, Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar da wasu gagaruman sauye sauyen tattalin arziki wanda gwamnatin da hukumomin lamuni na duniya suka ce sun zama wajibi a aiwatar domin daidaita harkokin kudade a kasar mafi yawan jama'a a Afirka.
Sauye sauyen dai cikin kankanin lokaci sun janyo faduwar darajar Naira da tashin farashin mai man fetur da ya rubanya har sau biyar.
Tashin gwauron zabi na farashin kaya a kasar ya kai kashi 34 cikin dari a bara yayin da a cikin watan Mayu Bankin Duniya ya yi kashedin cewa tattalin arzikin kasar na cikin garari.
A shekarar 2024 Bankin duniya ya yi kiyasin cewa kusan rabin al'umar Najeriya na fama da kangin fatara da talauci.