Tinubu ya duba wadanda rikicin Benue ya ritsa da su
June 18, 2025Ziyarar ta shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ta kasance wata dama ta sauraren al'umomin jihar Benue da suka hada da sarakunan gargajiya, waddanda suka taru a babban dakin taro na gidan gwamnati. Kabilun jihar Benue da shugabanin matasa sun samu zarafin gaya wa shugaban kasar halin da jihar ke ciki.
Karin bayani: Manoman Benue na neman a magance matsalar tsaro
Sai dai a martaninsa, shugaba Tinubu ya nuna bakin cikinsa ganin cewar maimakon zuwa Benue don kaddamar da ayyuka, ya je ne don jaje game da rasa rayukan al'umma da dama. Shugaba Tinubu ya ce: "Wannan ba irin ziyarar da nake son yi ba ne a jihar Benue. Ya kamata in zo ne domin kaddamar da ayyukan raya kasa. Amma abin takaici, gashi ina ziyara cikin yanayi na alhini, da bakin ciki. Za mu yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin cewar wannan yanayin da ake bai ci gaba ba."
A jawabin da ya gabatar, basarake Tor Tiv James Otese, ya dora laifin tashin hankalin jihar Benue ne kan makiyaya da ke neman mamaye kasarsu. Kasancewar ana neman maslaha ne kan wannan lamari, shugaban kungiyar makiyaya Miyetti Allah reshen jihar Benue Ardo Risku Mohammed, ya ce sun samu gayyatar shiga taron masu ruwa da tsaki.
Karin bayani: Sabon yanayi na tabarbarewar tsaro a Najeriya
Kananan hukumomin jihar Benue tare ne ke fuskantar matsalar tsaro, inda tun cikin watanni uku baya, aka soma fuskantar asarar rayuka da dukiyoyi, baya ga kafa sansanonin 'yan gudun hijira fiye da 20 a jihar. Kuma manyan jami'an gwamnatin kasa da suka hallara a jihar ta Benue sun hada da sakataren gwamnatin tarayya George Akume, gwamnonin jihohin Arewa ta Tsakiya, minstoci, tsaffin gwamnoni, 'yan majalisar kasa, mai ba wa shugaban kasa shawara kan harkokin saron Nuhu Ribadu, da shugabanmin rundunonin tsaro tare da kusoshin gwamnati.