Taɓarɓarewar dangantaka a tsakanin Turkiyya da tarayyar Turai
September 18, 2011Ƙasar Turkiyya ta yi barazar katse duk wata hulɗa tare da tarayyar Turai - idan har ƙungiyar ta kyale Cyprus ta karɓi ragamar shugabancin karɓa-karɓa a cikin ta - baɗi idan Allah ya kaimu gabannin warware taƙaddamar da ta shafi rarrabuwar tsibirin. Sashen tsibirin dake Girka dai na da wakilci a cikin ƙungiyar tarayyar Turai tun a shekara ta 2004, kuma ƙungiyar na shirin baiwa sashen ragamar shugabanci a watan Yulin shekara ta 2012.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar Turkiyya na Anatolia ya ruwaito mataimakin firaministan ƙasar ta Turkiyya Besir Atalay yana cewar, ɗaukar matakin zai janyo cikas ga dangantakar dake tsakanin ƙasar sa da ƙungiyar tarayar Turai. Cyprus dai ta rarrabu ta hanyar ƙabilanci tun bayan da dakarun ƙasar Turkiyya suka mamaye tsibirin, kana suke ci gaba da kasancewa a yankin arewacin tsibirin a matsayin martani ga juyin mulkin da mahukunta a birnin Athens suka tallafa a Nikosia da nufin haɗewa da ƙasar ta Girka.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu