Salon rayuwa
Taɓa Ka Lashe 15.07.2025
Abdulrahman Kabir M. Ahiwa
July 15, 2025Talla
Akwai Larabawa ‘yan asalin kasashe hudu da harkokin kasuwanci ya kai su Najeriya har kuma suka sami damar zama a jihohin Kano da Jigawa. Wadannan dai su ne Larabawan Libiya da na Yemen da na Lebanon da kuma na Siriya. Larabawan Libiya ne suka zauna a wasu sassan birnin Kano bayan shigowarsu kasuwanci irin na "Trans Sahara Trade".