Tawagar masu bincike a tsaunukan Tibesti
Wani masanin kimiyyar kasa a katon filin da ya kai murabba'in kilomita 100,000 mai ramuka saboda aman wutar duwatsu. Stefan Kröpelin ya je tsaunin Tibesti na arewacin Chadi domin yin binciken yanayin Sahara da ke gurin.
Tsauni mafi tsaho a yankin Sahara
Mai tsahon mita 3,445 tsaunin Tibesti na zaman mafi tsaho a yankin Sahara. Makonni hudu masu bincike daga jamai'ar Kolon ta kasar Jamus suka kwashe suna tafiya a tsaunin, daya daga cikin wurare da a baya-bayan nan aka gano a duniya. Masu binciken na son gano yadda mutanen yankin suka je Turai shekaru 100,000 da suka gabata da kuma rawar da yanayi ya taka ga masu hijirar.
Mafarkin mai bincike ya zama gaskiya
Jagoran masu binciken masani Stefan Kröpelin, ya ce rikicin siyasa a Chadi ya kawo cikas a binciken har sai a karshen shekarun 1990 suka kammala. Ya kagu ya samu wannan dama tsahon shekaru. "Muna da shaida a kan tauraruwa mai wutsiya da ke da nisan kilomita miliyan 500 domin ganin abin da aka yi, sai dai ba mu taba tantance duwatsun da ke kan tsaunin na yanki hamada mafi girma a duniya ba."
Bardai, babban birnin Tibesti
Abin da masu binciken ke son cimma shi ne isa Emi Kussi, babban gari a yankin. Sai dai a karshen watan Fabarairu na 2015, tawagar masu binciken da farko ta tafi Bardai da ke arewa maso yammacin Chadi. Babban birnin Tibesti, yankin da aka kirkira a shekara ta 2008 na da mazauna 1.500. Daga nan tawagar ta su ta karasa yankin Tibesti da babu kowa a ciki.
Taimako daga al'ummar yankin
Tawagar ta samu rakiyar al'ummar yankin da suka hadar da direbobi hudu da mai dafa abinci. "Da farko mun tsammaci mutane a nan na da tsaro sosai," a cewar Adam Polczyk, mai daukar hoto kuma jami'in yada labarai na masu binciken. "Sai dai daga bisani lamarin ya sauya nan take, kasancewar mu Turawa ba ma yin tafiyar gaban kanmu, mun zabi wasu al'ummar yankin su yi mana rakiya."
Hutawa a karkashin bishiyar gawo
Mafi yawan bangaren tafiyar an yi ta ne da mota kirar jeep. A ko da yaushe direbobin na duba inda ya kamata a huta domin kauce wa tsananin zafin rana. Gawo ne kadai bishiyoyin da ke samar da inuwa a lokacin tsananin zafin rana cikin kasa.
Ramukan da amon wutar dutse ya haifar, 'natron hole'
Domin yin gwajin farko, tawagar masu binciken ta fita daga mota. Jakuna sun dauki kayan aikinsu zuwa nisan mita 800 cikin yankin da ake fama da amon wutar duwatsu. Masu binciken sun kwashe tsahon yini guda da rabi kafin su isa gurin da ake kira da 'trou au natron.' Sunan 'natron hole' ya samo asali ne daga farar laka mai kyalli da santsi ta sinandarin Sodium da ta rufe wani bangare na ramukan.
Alamomin tafki
Stefan Kröpelin ya samu burbushin busasshiyar laka a yankin na 'trou au natron" kuma wannan burbushin na nuni da cewa, an taba samun kogi a wajen a shekarun baya. Ya na da wahala a hakikance hakan, ai dai gaskiya ne cewar shekaru 5,000 zuwa 10,000 da suka gabata yankin Saharar ya kasance korama.
Farko korama daga bisani Sahara
An samu tabbacin hakan daga wani kogo mai dinbin tarihi da masu binciken suka gano a tafiyar ta su. Dabbobi irin su Karkanda da Giwaye da Kunkuru da kuma Dorina sun zauna a wannan yanki da yanzu ya kasance wuri mafi bushewa da rashin danshi a doron kasa.
Tsallake hamada
Bangare na biyu na binciken ya kai masu binciken zuwa gabashin kasar. Tawagar ta kwashe tsahon yini biyar tana tafiya a hamada kafin tsallakawa zuwa Emi Kussim, inda suka kudiri aniyar zuwa. "Yankin hamada na zaman hanyar da bakin haure ke bi zuwa nahiyar Turai gabanin tarihin dan Adam," a cewar masanin kimiyar kasa Stefan Kröpelin. "Kuma dole ne sai sun bi ta Emi Kussi."
Hawa tudu cikin wahala
Da farko sun dauki wata hanyar tafiya mai wahala. A wannan karon sun yi amfani da rakuma maimakon jakuna. "Abin mamaki ne ganin yadda tawagar dabbobin ke hawa kan tsaunin mai wahala," a cewar mai daukar hoto polczyk. "Sun kai iya inda karfinsu zai iya kamar yadda muma muka kai."
Wuri mai abin al'ajabi
Bayan da ya isa saman tsaunin, Stefan Kröpelin ya dauki samfur domin yin gwaji. Bayan da ya dawo Jamus dole ne ya yi hakuri domin sakamakon binciken a dakin gwaje-gwaje na dadewa bai fito ba. Sai dai Kröpelin ya ce ya samu nasara a binciken da kuma kwarewa da ba zai manta ba: "Wurin na da matukar ban al'ajabi da ya sa na ke ganin Tibesi ka iya zama wani yanki na tarihi a duniya nan gaba.
Abokantaka a sansanin jin dumi
Tafkin Ounianga na daya daga cikin wuraren da hukumar UNESCO ta Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsyin wuraren tarihi na duniya. UNESCO na kuma duba Ennedi Plateau. Kröpelin ya ce ya kamata a sanya Tibesti "Ina yin kira ga al'ummomin kasa da kasa su dauki matakin inganta rayuwar mazauna yankin, ina fatan ganin hakan." Da haka ya ke fatan biyan mazauna gurin taimakon da suka yi musu.