Ana neman a yi mana kazafi a zargin rusa kungiyarmu da gwamnatin Nijar ta yi, in ji Moussa Mahamadou mataimakin babban magatakarda na kungiyar alkalan Nijar ta SAMAN. Jim kadan bayan wannan tattaunawa dai, sojojin da ke mulki a Jamhuriyar Nijar din suka sauke shi daga alkalancin.