Tattalin arzikin Turai ya bunkasa
April 30, 2025Kasashen Turai masu amfani da kudin Euro sun samun bunkasa na tattalin arziki a farkon wannan shekara ta 2025, fiye da hasashen da aka yi, duk da matakin kakaba harajin kayayyakin da ake shigarwa zuwa Amurka na Shugaba Donald Trump.
Karin Bayani: EU za ta yi wa shugaba Trump na Amurka martanin karin haraji
Alkaluman bayanai da aka fitar sun nuna cewa kasashen 20 da suke amfanin da kudin bai daya na Euro sun samun bunkasa na tattalin arziki da 0.4 cikin 100 tsakanin watan Janairu zuwa Maris na wannan shekara ta 2025. Sannan kuma a gaba daya tatalin arzikin kasashe 27 da ke cikin kungiyar Tarayyar Turai ya samu bunkasa ta kaso 0.3 cikin 100.
Wannan duk da yanayin tarnakin kasuwanci da ake fuskanta a duniya kan kara kudin fiton shigar da kaya zuwa kasar Amurka, wadda take matsayi na farko na karfin tattalin arziki tsakanin kasashen duniya.