Tatalin arziƙin ƙasashen Turai
May 9, 2012Talla
Merkel ta yi wannan kiran ne bayan da wannan yarjejeniya da su ka cimma ke ƙoƙarin cin karo da cikas sakamakon kiran da shugaban Faransa mai jiran gado Francois Hollande ya yi na cewa a sake duba yarjejeniyar da nufin yi mata gyaran fuska.
Shugabar ta gwamnatin Jamus ta ce muddin yarjejeniyar ta sami ci baya to kuwa akwai yiwuwar tattalin arziƙin kasashen ya shiga hali na tsaka mai wuya.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Halima Balaraba Abbas