Tasirin janye tallafin Amurka a yaki da Malaria
April 25, 2025Ya zuwa shekaru biyu baya dai kaso kusan 97 cikin dari na al'ummar tarayyar Najeriya miliyan 200 da doriya sun kamu da cutar zazzabin cizon sauro.
Kaso kusan 30 a cikin dari na kamuwa da cutar sauron a duniya dai na faruwa ne a tarayyar Najeriyar kasar da ke dogaro da tallafin kasashen waje wajen baban yakin da kan hallaka mutane kusan 200,000 a shekara.
Ya zuwa watan Mayun bara kadai cibiyar USAID ta bada agajin dalar Amurka miliyan 914 ga tarayyar Najeriya domin yaki da zazzabin cizon sauro a shekaru 13 , agaji mafi yawa a bangaren kasashen waje kafin matakin shugaba Trump na dakatar da aiyyukan cibiyar.
Janye tallafin cibiyar kasar Amurka ta USAID dai daga dukkan alamu na zaman barazana mafi girma a cikin yakin da ke zaman barazana ta kan gaba cikin batun lafiya a Najeriya.
Koma ya zuwa ina masu mulkin ke fatan iya rage radadin zare tallafin, daga dukkan alamu zare tallafin na shafar kokarin kai cutar sauron zama tarihi.
Koma ya zuwa ina janye tallafin ke iya kai wa ga kara ta'azzarar cutar cizon sauron dai Najeriyar na fatan wani rigakafin cutar da ma kila dalar Amurka miliyan 200 da tarayyar Najeriyar ta ciwo bashi na iya kai wa ya zuwa rage tasirin zazzabin tsakanin yara kanana da kila mata masu ciki.
Ya zuwa karshen shekarar bana dai tarayyar Najeriya na da babban burin rage yawan kamuwa da zazzabin cizon sauron da akalla kaso 50 cikin dari cikin kowanne yara 1000 da ke kasar.