Tashe-tashen hankula sun ta'azzara a Siriya
April 30, 2025Jakadan musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Siyara, Geir Pedersen ya yi tir tare nuna takaicin tashin hankalin da ake ci gaba da samu ba a kasar ta Siriya na rikicin tsakanin bangarorin al'umma sannan jami'in ya bukaci ganin kawo karshen jhare-haren ta sama na dakarun Isra'ila kan kasra ta Siriya.
Karin Bayani:Neman dubban 'yan Siriya da suka yi bace
Jami'an na Majalisar Dinkin Duniya, Geir Pedersen ya ce akwai firgitarwa bisa yadda tashe-tashen hankula suke fadada a kasar Siriya musamman a yankunan Damascus babban binrin kasar da birnin Homs sannan Isra'ila tana kai hare-hare kusa da babban birnin kasar.
Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila ya ce sojojin kasarsa sun dauki matakin ne domin kariya, saboda yuwuwar rikicin na Siriya ya fantsama zuwa kasarsa. Fararen hula da dama wannan rikici na Siriya ya shafa.