Tashe-tashen hankula sun halaka mutane dubu-10 a Najeriya
May 29, 2025A wannan Alhamis wani rahoton kungiyar Amnesty International ta kasa da kasa ya ce tashe-tashen hankula da ake fuskanta daga kungiyoyin masu kaifin kishin addinin Islama da tsageru masu aikata laifuka sun halaka fiye da mutane dubu-10 cikin shekaru biyu da suka gabata, a yankunan tsakiya da arewacin Najeriya.
Karin Baynai: Najeriya: Zanga-zanga na daukar sabon salo
Rahoton ya daura alhakin abin da ke faruwa kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wadda ta gaza kare mutane daga hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadi, tun lokacuin da ya dauki madafun iko shekaru biyu da suka gabata.
Ita dai kungiyar Amnesty International ta fitar da rahoton yau Alhamis da gwamnatin Shugaba Tinubu ta cika shekaru biyu kan madafun ikon kasar ta Najeriya mafi yawan mutane tsakanin kasashen nahiyar Afirka.