Taron Tarayyar Turai kan tattali
June 28, 2012A yayin taron, ana saran shugabannin Italiya da da Faransa da spaniya, zasu yi matsin lamba wa Jamus dan gane da bukatar ta amince da tsarin raba bashi, kafin halin da kasuwanni ke ciki ya rusa tattalina arzikin kasashen dake amfani da kudin Euro. Bayan ganawarsu a birnin Paris, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaba Francois Hollande na Faransa, sun cimma yarjejeniyar bukatar euro biliyan 130 a matsayin kudaden ceto, kamar yaddashugaban Faransan ya nema, sai dai hakan na mai kasancewa tamkar kuɗaɗen da tarayyar turan ke dashi ne a kasa. Masu zuba jari da kasuwannin hada-hada dai na bukatar sanin mafita cikin wannan makon, domin tabbatar da cewar matsalar basussuka da wasu ƙasashen turan ke ciki , bazai durkusar da tattalin arzikin duniya ba. Sai duk da wannan matsayi nasu, basa kyautata zaton za'a warware wannan matsala, amma duk sun yi amanar cewa komai ya ta'allaka ne da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu