Taron shugabanin Turai a Brussels
June 29, 2012A yayin da ake sa ran kammala taron ƙoli na ƙungiyar Turai a wannan juma'ar, Shugabanin ƙungiyar da ke ganawa a birnin Brussels sun amince su yi amfani da kuɗin tallafinsu wajen ƙarfafa hannayen jarin bankunan da ke tangal-tangal.
Shugaban kwamitin zartarwar ƙungiyar Herman Van Rompuy ne ya bada sanarwar wannan shawara da suka yanke.
Wannan yarjejeniya ta zo ne bayan da ƙasashen Italiya da Spain suka tilata gudanar da tattaunawar har cikin daren alhamis, bayan da suka ƙi su sanya hannu, kan yarjejeniyar da shugabanin suka yi kan wani shirin samar da bunƙasar tattalin arziƙin ƙasashen Nahiyar.
Kasashen biyu sun buƙaci da a dauki matakin gaggawa dan rage yawan basussukan da ke kan su.
Van Rompuy ya faɗawa manema labarai cewa shugabanin ƙasashe 17n masu amfani da takardar kudin euro sun kuma amince da wata hukuma ta haɗin gwuiwa wacce zata riƙa sanya ido kan harkokin bankunan kuma ƙungiyar mai ƙasashe 27 ta yarda da matakan ƙarfafa haɗin kai a fuskar siyasa da kuma sanya ido kan kasafin kuɗin ƙasashen
"Ƙarfafa jarin bankunan Turai da Euro milliyan dubu 10 zai ƙara mata ƙarfin ba da rance da milliyan dubu 60 kuma wajibi ne wannan kudi ya gangara zuwa ƙasashen nahiyar ya kuma taimaka wa kamfanoni ta yadda zasu fitar da kansu daga wannan rikicin kudi"
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Halima Balaraba Abbas