Taron shekara na Majalisar Dinkin Duniya
September 25, 2012A birnin New-York na Amurika an buɗa taron shekara-shekara na Majalisar Dinkin Duniya.Rikicin Siriya na daga mahimman batutuwan da mahalarta taron ke tattanawa akai.
A jawabin da ya gabatar, jakadan Majalisar Dinkin Duniya a Siriya Lakhdar Brahimi, ya buƙaci gamayyar ƙasa da ƙasa ta ƙara azama wajen laluben hanyoyin warware rikicin ƙasar.
Lakhdar Brahimi yayi jawabin nasa a cikin wani yanayi na kariyar zuciya, inda ya nuna halin ƙunci da al'umar Siriya ke ciki.
Bayan ga dubunnan mutanen da suka rasa rayuka, dubun-dubbunai sun shiga halin gudun hijira, ga kuma uwa uba bala' in yinwa da ƙasar ta faɗa a ciki, kuma har kulum wutar rikici nakara ruwa.
Lakhadar Brahimi ya ce ya rumtse ido bai ga kyan makamta ba,game da gano bakin zaren warware rikicin Siriya:
"A yanzu ba ni da wani tsari na magance rikici saidai ina da shawarwari, wanda idan ɓangarorin da abun ya shafa za su amfani da su, ba shakka za su taimaka a samu mafita.Shawarwarin sune na gabatarwa Majalisar Dinkin duniya."
Brahimi ya kai ziyarce-ziyarce a ƙasashen Masar, Lebanon da Siriya, inda ya gana da masu ruwa da tsaki a wannan rikicin, ya baiyanawa Majalisar Dinkin Duniya wasu daga shawarwarin da ya bayar:
"A Damakus da duk sauran wuraren da na ziyarata na baiyana masu cewa Siriya na buƙatar cenji na zahiri daga ɓangarori daban-daban.Cimma masalaha irtin ta gobe a dawo, ba za ta kawo ƙarshen wannan rikici ba.To amma kai wa ga wannan mataki cilas sai an samu goyan bayan kowa.Idan wanan ko wacen ɓangare na Komitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya yayi tsaye kan ra'ayinsa,Siriya za ta ci gaba da kasancewa cikin wannan mummunan yanayi.Sannan idan ta kasance ni da Majalisa ta ɗorawa yaunin shiga tsakanin rikicin ban samu haɗin kai ba daga dukan membobin Komitin Sulhu matsayina bai da amfani".
Lakhadar Brahimi, ya yi kira da babbar murya ga gamayyar ƙasa da ƙasa ta ƙara himmantuwa a ƙoƙarin kawo ƙarshen rikicin Siriya.
Har dai ya zuwa wannan lokaci ana fuskantar saɓanin ra'ayi a tsakanin membobin Komitin Sulhu bayan da ƙasashen Rasha da China suka hau kujerar naki a kudururukan da komitinya gabatar domin hukunta gwamnatin Siriya.
Ministan harakokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya yi kira ga ƙasashen biyu su gama ƙarfi da gamayyar ƙasa da ƙasa domin samun masalaha, Westerwelle ya ce cilas ne aƙara a zama wajen kuɓuto al'umar Siriya
"Idan muka yi sako-sako na rikicin Siriya, tamkar muna ƙara saka jama'ar ƙasar ne cikin masifa.Mu duka munsan ƙuncin rayuwa da jama'a ta shiga.Lalle ba mu za mu iya samun masalaha ba cikin ɗan ƙanƙanan lokaci, to amma idan mu ka nuna halin ko inkula wankin hula zai kai mu dare."
Baici rikicin Siriya, taron Majalisar Dinkin Duniya na wannan shekara nan a manyan ajendodi a gabansa, wanda suka haɗa dabatun girka 'yanttanciyar ƙasar Palestinu da kuma faifen Video da wani bayahuden Amurka ya shirya inda ya tozarta addinin Islama.Hakazalika mahalarta taron,za su masanyar ra'ayoyi game da jalin da ƙasar Mali ta shiga.
Mawallafa:Schmidt Thomas/Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Alyi