Taron ministocin kuɗi na ƙungiyar Tarayyar Turai
November 8, 2011Ministocin kudi na ƙungiyar ƙasashen Tarrayar Turai waɗanda suka kammala wani taro a a birnin Brussels sun jinkirta bayar da tallafi ga ƙasashen Girka da Italiya tare ma da ƙara ƙarfafa asususun tsumi na ba da agaji ga ƙasashen da ke fama da mtsalar tattalin arziki .
Wannan sanarwa da ministocin suka baiyana a ƙarshen taron ta zo ne a daidai lokacin da gwamnatin Girka take faɗi tashin kafa gwamnatin gambiza, tare da neman ganin tsohon fraministan George Papandreou ya salama muƙamin. Ministocin waɗanda suka samu rarrabuwar kawuna wajan cimma matakin bai ɗaya da zai kai ga tallafawa ƙasasshen Girka da Italiya, sun ce zasu ƙara yin wata tattaunawa a ƙarshen wannan wata da nufin daidaita al'ammura.
Buƙatar ƙasashen ƙungiyar EU ga hukumomin ƙasar Girka
Sai dai sun yi kira ga yan siyasar na ƙasar ta Girka da cewar da zaran sun sani nasarar kafa gwamnatin riƙon ƙwarya to za ta sa hannu akan wata yarjejeniya domin yin aiki da shawarwari da aka cimma na shirin tsuke bakin aljihun a karshen watan jiya, abinda zai ba su damar samun zagaye na biyu na kuɗaɗen tallafin da za su kai Euro biliyan dubu takwas. Babban kwamishinan ƙungiyar Tarayyar Turai Oli Rehn ya ce tilas ne sabbin shugabannin ƙasar na Girka su ɗauki alƙawari a rubuce a gaban hukumomin kuɗi na EU da IMF cewa kafin a basu gudunmowar, sannan kuma ya ƙara da cewar mu daga ɓangaran mu mu yi abinda ya kamata mu yi; yanzu ya rage ga Girka ta yi nata bangaren, kuma ba na tsamanin cewar ni kadai ne ke da ra'ayin cewar yin ƙuria'ar raba gardama akan shirin na tsuke bakin aljihu ya sabama yarjejeniyar da muka cimma tun ranar 27 ga watan oktoban da ya gabata.
Fargaban ƙasahen ƙungiyar Tarayyar Turai akan ƙasar Italiya
Ministocin kuɗin na ƙasashen ƙungiyar sun ce suna da babbar fargaba akan Italiya baya ga ƙasar ta Girka don haka suka umurci ƙasar da ta gaggauta ƙaddamar da sauye sauyen tattalin arziki wanda gwamnatin ta baiyana tun a cikin watan Satumba. A halin da ake ciki fargaban da ƙasar ta Italiya ta ke da shi akan masu saka jari dangane da giɓin da ta ke fama da shi ya fara zama abin tsoro wanda ma shi ya sa ta buƙaci manyan sipetocin hukumar tsara kuɗaɗen na IMF da kuma EU da su sa ido akan tattalin arzikin ƙasar sannan kuma ga faduwar farashin hannayan jari.
Jean Claude Juncker shine shugaban tawagar ministocin, wanda kuma yace ya kamata su sani cewar ya na da wahala mu shawo kan al 'umma a cikin ƙasashen Jamus da Holland da Beljium da Austriya da kuma Luxemburg na su ba da hadin kai ba tare da Girka ko Italiya sun tanadi matakai ba da zasu kare darajar kudin Euro. Yace karshe na yi farin ciki bayan watannin na kokarin ya siyasar Girka sun yarda su ba da hadin kai, kuma yace abinda ya kamata a ce an yi kenan tun da daɗewa.
Nan gaba ne ƙasashen ƙungiyar za su tsaida shawara akan ƙara ƙarfafa asusun ko ta kwana na agazawa ƙasashen, wanda zai ƙumshi aƙalla Euro biliyan dubu ɗaya domin ceto ƙasashen da bashi ka iya yiwa katutu.
Mawallafi :Abdourahamane Hassane
Edita :Usman Shehu Usman