Taron ministocin ƙasashen Turai a Brussels akan Haiti
January 26, 2010A yayinda ƙasashen Duniya keci gaba da gangamin kai kayan agaji zuwa ƙasar Haiti domin tallafawa al'umar ƙasar da suka jigata a sakamakon girgizan ƙasar daya halaka kimanin mutane Dubu 150. Ministocin harkokin wajen ƙungiyar tarayyar Turai sun amince da sake aika ƙarin 'Yansanda 300 domin talafawa dakarun majalisar Ɗinkin Duniya a ƙasar.
Bayan taron ministocin harkokin wajen ƙungiyar ta Tarayyar Turai da aka kammala jiya a birnin Brussels. Ministocin sun amince da ƙara tura dakarun 'yan sanda 300 zuwa ƙasar ta Haiti da zummar tallafawa aikin dakarun Majalisar Ɗinkin Duniya dake aikin wanzar da zaman lafiya da kuma aikin jinƙai a ƙasar.
Ɗaukan wannan mataki na tura ƙarin jami'an tsaron, inji kwamishinan Raya ƙasashen ƙetare na ƙungiyar ta EU ya zama wajibi idan akayi la'akari da matsalolin da ake fuskan yanzu haka a haitin. Yace: Harkokin gudanar da gwamnati a Haiti ya taɓarɓare, komai ya tsaya cik , kuma wannan ba wai ya shafi gine-gine da suka ruguje ba, a'a harma da harkokin mulki sun tsaya:
Bayan matakin da EU ta ɗauka na tura ƙarin Yan sandan karo-karo, haka kuma zasu tura Injiniyoyi da jirage masu saukar angulu da jiragen Ruwa da kuma girgina Asibitoci. Fatan ƙungiyar ta EU dai shine samun haɗin kai daga ɓangarori daban-daban dake aikin samar da agaji zuwa ƙasar ta Haiti.
Yanzu haka dai daga cikin Yan Sandan da za'a tura ƙasar ta Haiti, Italiya zata aika da Yan sanda 120 zuwa 150, sai faransa da zata aika da guda 100, sai Holland mai 60 a yayinda Spain zata aike da 'yansanda 25 zuwa 30.
A wani taro makamancin wannan da akayi a ƙasar Canada da zummar taimakawa ƙasar ta Haiti, Firaministan Canada Stephen Harper yace zai ɗauki shekaru kimanin 10 kafin a sake gina ƙasar ta Haiti. A saƙon daya aike wajen taron shugaban Obama ya ƙara jaddada ƙudirin gwamnatin sa taimakawa Haiti. Obama yace: bada taimako ga ƙasar dake fama da irin wannan bala'i zaici gaba da zama mahinmin abinda ƙasar mu zata maida hankali. Zamuyi anfani da hanyoyin soji da difilomasiya da kuma ƙwarin guiwa irin na al'umar mu na taimakawa:
Bayan batun ƙasar ta Haiti ministocin ƙasashen ƙetaren sun kuma taɓo batun ƙasar Afghanistan,musanman batun taron da za'a gudanar a ranar alhamis mai zuwa a birnin London. A lokacin taron ministan harkokin wajen Sweden Carl Bildt yayi bayani yana mai cewar yace: bana fatan zamu ajiye wata ranar ficewa daga ƙasar. Munaso ne mu ɗauki matakan janyewa na sannu a hankali daga samar da tsaron soji zuwa na faran hula, amma duk wani batun janyewa a yanzu zai zama riba ne ga ƙungiyar Taliban:
Mawallafi: Babangida Jibril
Edita: Mohammad Nasir Awal