Taron kolin shugabannin EU da Afirka ta Kudu
March 14, 2025Shugabannin EU da Afirka ta Kudu sun baiyana cewa babu wanda ya kai Ukraine da al'ummar kasar bukatar zaman lafiya, kasancewar zaman lafiya, yafi zama ‘dan sarki.
Afirka ta Kudu na kasancewa farin wata sha kallo a da'irar diflomasiyya da kuma wanzar da zaman lafiya a duniya, rawar ke nan da take takawa a yakin Rasha da Ukraine, duk da cewa Pretoria na cikin wadi na tsaka mai wuya wajen kulla kawance da makiya biyu da ke filin daga. Shgaba Cyril Ramaphosa ya ce kasarsa za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta bada gudummuwa 100 bisa 100 don kawo karshen yakin Rasha da Ukraine.
Karin Bayani:Afirka ta Kudu ta amshi ragamar shugabancin G20
Shugaba Ramaposa ya ce hakika mutanen Ukraine, har ma da na Rasha na matukar bukatar zaman lafiya fiye da kowane mahaluki a duniya, kuma aikin mu shi ne karfafa musu gwiwa wajen lalubo bakin zaren kawo karshen wannan yaki. Wannan ne sakon da zan sanar da shugaba Zelenskiy idan ya zo nan, kuma bukatar da zan ci gaba da mikawa ke nan ga shugaba Putin, domin dukkanin kasashen na da rawar da za su taka wajen kawo karshen yakin.
Shugabar Hukumar gudanarwar Kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta bukaci sake fasalta hanyoyin diflomasiyya wajen warware takaddamar da ke tsakani a yakin Ukraine.
Karin Bayani:Von der Leyen na ziyara a Afirka
"Mun yi musayar ra'ayoyi da shawarwari wanda zai kai ga amincewar dukkan bangarorin na mayar da wuka cikin kube, domin a samu zaman lafiya ta dundundun, ba wai kawo karshen yakin ba, har ma da kulla amana ta gaskiya wajen cimma yarjejeniyar zaman lafiyar.
Baya ga tattaunawa kan yakin Ukraine, kungiyar EU ta sanar da zuba jarin sama da Euro biliyan €4.7 kwatankwacin Dala biliyan ($5.10) ga Afirka ta Kudu. EU na son fadada cinikayyarta da sabbin kawaye wajen kulla yarjejeniyar kasuwanci mara shinge da zuba hannun jari tsakanin kasashen.
Karin Bayani:Iskar gas na Afirka zuwa Turai
"Tarayyar Turai ta kasance abokiyar hulda mafi girma ga Afirka ta Kudu. Mun zo ne domin kaddamar da wannan gagarumin shiri na zuba hannun jari, wanda Afirka ta Kudu ce kasa ta farko da ta samu irin wannan tagomashi, ta hanyar rattaba hannu kan wannan yarjejeniya.
Karin Bayani: Trump ya yi barazanar katse zuba Jari a Afirka ta Kudu
EU da kasar Afirka ta Kudu na fuskantar matsin lamba daga fadar White House na Amurka, dangane da manufofin gwamnatin Trump kan haraji da tattalin arziki da makamashi da sauyin yanayi da kuma bambancin ra'ayin kan yakin Ukraine.