Taron kolin Kungiyar Tarayyar Turai
December 9, 2011Shuwagabanin Kungiyar Tarayyar Turai sun amince da wani sabon mataki na tsaurara dokokin kasafin kudin kasashen. To sai dai a wani abun da ke zaman masu koma baya, sun gaza amincewa da kwaskware wasu daga cikin dokokin da ke yarjejeniyar da ta kafa kungiyar, bayan da Frime Ministan Burtaniya David Cameron ya kalubalanci tayin da kasashen Jamus da Faransa suka gabatar. Frime minista Cameron, ya ce cibiyoyin kungiyar, mallakar kasashe 27 da ke mambobinta ne kuma sauya yarjejeniyar ba ita kadai bace hanyar fita daga matsalar bashin. Shuwagabanin kasashe 27 da ke Tarayyar suna gudanar da wata ganawa ta wuni biyu a Brussels. Shugaban Majalisar zartarwar kungiyar Herman Van Rompuy a wannan juma'ar ya ce rukunin kasashen da ke amfani da takardar kudin euro wanda ke da mambobi 17, da kuma wasu kasashe shidda da ke zaman mambobin uwar kungiyar sun amince da sabon yarjejeniyar kasafin kudin, kuma shawarwarin wannan yarjejeniya sun tanadi sanya takunkumi kai tsaya a kan kasashen da suka kashe kasafin kudin da ya fi karfinsu. Van Rompoy ya ce ya so a ce an amince da daukar mataki na bai daya wajen kwaskware yarjejeniyar Turan to amma lokaci ya riga ya kure.
Mawallafiya: Pinado Abdu
Edita : Umaru Aliyu