Taron kawo karshen yakin Ukraine a Landan
March 2, 2025Da yake jawabi bayan taro kasshen Turai a kan Ukraine, firaministan Burtaniya ya bukaci kasashen duniya musamman ma manyan kawayen Ukraine da su hada kansu wajen ganin sun taimaka an kawo karshern wannan yaki na shekaru uku.
Taron wanda ya kunshi shugabannin kasashen Faransa da Jamus da Italiya da Denmark har ma da na Turkiyya, da jagorancin kungiyar Tarayyar Turai da na kungiyar tsaro ta NATO ya sha alwashin tallafawa Ukraine da makudan kudade domin sayen makaman kare kanta.
Kazalika taron ya kuma tattauna batun fargabar ko Amurka za ta janye tallafinta ga kungiyar NATO, kasashen Turai sun ce lokaci ya yi da zasu fara dogaro da kansu.
Starmer ya ce ganin yadda tattaunawar Zelensky da Donald Trumpta kaya a fadar White House, babu wanda zai so a ce da shi ne hakan ta faru da shi.
Karin Bayani: Kasashen EU na taron cika shekaru uku da fara yakin Ukraine