TARON KASASHEN KUDANCIN TURAI DA AREWACIN AFRIKA
December 5, 2003Talla
Yau ne aka bude taron yini biyu na kasashen dake kudancin turai biyar da wasu biyar na arewacin Afrika a kasar Tunisia.Muhimman batutuwa dake daukan hankalin mahalarta wannan taro shine batun hadin kai tsakanin kasashen dake yankin Mediterian,yaki da danne yancin biladama,tare da batun barazanar harkokinmasu tsattsauran raayi na addini Islama. Ayayinda shugabannin kasashen Algeria,Libya,Murtania da Morocco da mai masaukin baki Tunisia, wakilan kungiyar Maghreb na Larabawa,suka hade da Faransa,Italia,Malta,Portugal da Spain a birnin Tunis,ana saran zasu tattauna matuka gaya kann wadannan batutuwa dake barazana ga zamantakewansu.
Shugaba Jacques Chirac na Faransa ,da Zine al Abidine Ben Ali,tuni suka isa Tunisia don bude wannan taro,ayayinda tun a jiya alhamis ne Sarki Mohammad na 6 na Morocco,Moamer Ghadafi na Libya da Shugaba Abdelaziz Bouteflika suka isa Tunisia dangane da wannan taro na yini biyu.Sauran mahalarta taron sun hada da Prime ministan SpainJose Maria Aznar dana Italiya Silvio Berlusconi.
An dai dauki tsauraran matakai na tabbatar da tsaron mahalarta wannan taro na kasashe 10 a birnin Tunis.Isowan shugaba Ghadafi da tawagarsa cikin jerin motoci daga Libya yaso ya kawo matsaloli wa jamian tsaro a birnin tunis. To sai dai gabannin wannan taro a jiya an samu rikice rikice tsdakanin kungiyoyin dake fafutukan kare hakkin biladama na kasar ta Tunisia.
Tunisia dai na mai zama daya daga kasashen da Amurka ke zargi da take hakkin biladama,tare da tarihin tura mutane kurkuku saboda sun nuna adawa da gwamnatin Ben Ali.A majalisar dokokin kasar mai jammiyyun siyasa masu yawa,yan adawa kadan ne keda wakilci,kana a shekara ta 1999 aka sake zaben Ben Ali da kuriu kashi 99 daga cikin darin wadanda aka kada.
Wata matsala kuma da ta taso a wannan taro shine batun kudin diyya da faransa ke nema daga Libya wa iyalan wadanda hadarin jirgin sama ya ritsa dasu a shekara ta 1989,a sararin samaniyan Niger.Harin jirgin daya kashe mutane 170,54 daga cikinsu kuwa yan faransa. An dai fara taron kasashen 10 tun daga shekarata 1990,wadda aka fara a matakan ministocin kasashen waje a Italy.Shugabannin dai zasu tabbatar da magance kwaroran bakin haure,matsalolin yan taadda,da kuma mayar da yankin wurin zaman lafiya da kwanciyan hankali.A gobe ne ake saran rufe taron idan mai duka ya kaimu.

Talla