Wasu kungiyoyi sun yi shelar kauracewa taron kasa na Nijar
February 13, 2025Yanzu haka dai birnin Yamaina ci gaba da daukar harami na tarben bakin dubu shida da 27 wadanda za su halarci babban taron mahawarar na kasa .
To Sai dai kuma a daidai loakcin da ya rage kwanaki kalilan a bude taron wasu manyan kungiyoyi da suka hada da kungiyar lauyoyin kasar Nijar da kuma ta ANLC reshen Transparancy a Nijar sun sanar da daukar matakin kaurace wa taron.
Ita ma dai kungiyar lauyoyi ta kasa ta ce za ta kaurace wa taron saboda ba amince da tsarin zaman taron ba da kuma wa'adin da zai dauka.
Sai dai hatta wasu kungiyoyi irin su SEDEL/DH Niger da ke goyon bayan mulkin na CNSP sun ce tayin da aka yi musu na zuwa taron a kai kasuwa.
Wani batun na daban da ke ci gaba da haddasa mahawara kan wannan taro na kasa shi e rashin gayyatar jam'iyyun siyasa ko kuma ma ‘yan siyasa a cikin taron.
A halin da ake ciki kwamitin kwararru da aka dora wa nauyin shirya wannan babban taron mahawara na kasa ya bayyana cewa ya zuwa yanzu dukkanin jihohi takwas na kasar ta Nijar har ma da mazauna kasashen ketare sun aiko da sunayen wakilansu da kuma shawarwarinsu na zuwa ga taron a rubuce.