Taron hukumar CNDP a Nijar
July 3, 2012A jamhuriyar Nijar kwamitin sasanta rigingimun siyasa ya kammala zaman taron sa a birnin Yamai inda ya tattauna kan batun kuɗaɗan tallafin da gomnati zai baiwa jam'iyyun siyasa na ƙasar da kuma batun sabinta rijistan zaɓe zuwa na zamani.
Taron ya kawo ƙarshe tare da ɗaukar wasu muhimman shawarwari;sai dai tuni ƙananan jam'iyyun siyasar ƙasar su ka koka da abin da su ka kira rabon kura da aka yi wajan kasafin kuɗaɗan tallafin.Taron wanda ya hada wakillan jamiyyun siyasa 61 na ƙasar ta Nijar a ƙarƙashin jagorancin framinista Briji Rafini ya soma ne da tattaunawa kan batun sabinta rijistan zaɓe ya zuwa na zamani da ba a iya yin na gogi ba da ake kira Biometrique a faransance.
bCece ku ce akan sabinta rejistan zaɓe izuwa na zamani
Malam Amadu Lawal Edmond daya daga cikin wakillan jam'iyyun siyasar da ya halarci taron ya ce tilas a sake rejistan zaɓen domin kaucewa yin maguɗi a zaɓuɓuka na gaba.
Batu na biyu da taron ya tattauna a kan sa shine na kasafin kuɗaɗan tallafin da gomnati ke bai wa jam'iyyun siyasa;a ƙarƙashin wata tsohuwar dokar da ta tanadi kasafa waɗannan kuaɗaɗe.A ko wace shekar gomnati za ta ware kashi 0 ,3 daga cikin ɗari na kuɗaɗan shiga na haraji da ta samu a shekara domin rarrabawa jam'iyyun siyasar dokar da taron ya sake yin nazarin ta tare da tsaida matakai:
#b#Ƙananan jam'iyyun siyasa na kokawa cewa an yi rabon kura na kuɗaɗe da ake bai wa jam'iyyun
To sai dai ƙananan jam'iyyun siyasa na ƙasar sun nuna rashin jin daɗinsu da matakin da taron ya tsayar kan wanann batu na kasafin kudin tallafin gomnati da su ka ce an yi kashin dankali a cikin shirin;Malam usmane alhaji ibrahim shine wakilin jamiyyar PMT Albarka ɗaya daga cikin ƙananan jam'iyyun ƙasar ta Nijar ya ce bai kamata ba a nuna banbanci wajan rarraba kuɗaɗen saboda ko wacce jam'iya ta na da haki dai da sauran jam'iyyun siyasar.
Tuni dai ƙananan jam'iyyun siyasar su ka rungumi kadara bayan da manyan jam'iyyun siyasar su ka rinjayesu a kan wannan batu a cikin zauran taron ;Daga ƙarshe taron ya ja hankalin gomnatin ƙasar Nijar kan ta gaggauta ɗaukar matakkan ware kuɗaɗen gudanar da wannan aiki na sabinta rijistan zaɓen tun da sauran lokaci.
Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto
Mawallafi : Gazali Abdu Tassawa
Edita : Abdourahamane Hassane