Taron ECOWAS a Abuja akan tsaro
February 16, 2012A ci-gaba da ƙoƙarin neman mafita a tsakanin ƙasashen yankin yammacin Afirka na ECOWAS da yanzu haka ke fuskantar ƙalubalen tsaro da ci-gaba, shugabannin ƙasashen yankin, a taronsu na Abuja suna da nufin ɓullo da sabbabin dabarun tunkurara rikicin dake barazana ga makomar yankin baki ɗayansa
Sun dai ta tafi da shewa na sake tabbatar da demokaraɗiyya da ma zaman lafiya a ƙasashe irin nasu jamhuriyar Nijar da Cote d'Ivoire da ma 'yar uwarta ta Gini.
To sai dai kuma wani ɓangare na sake shiga rukuki ga yayan kungiyar kasashen yankin yammacin Africa na ECOWAS da shugabanninta ke can ke taron su na shekara shekara cikin hali na tsoro da rashin tabbas.
Ga dai matsalar 'yan Boko Haram a tarrayar Nijeriya, da ma 'yan uwansu na yankin Niger Delta dake ci-gaba da kartar kasa dama rikiɗewa ya zuwa 'yan fashin da suka addabi ruwayen yankin Gulf of Guinea, sannan kuma ga tawayen Abzunawar da yayi aure ya tare a ƙasar Mali sannan kuma ke barazanar watsuwa zuwa makwabtan ƙasashen irin na su niger.
Abun kuma da yanzu haka ke tada hankula dama hakarkari ga shugabanin ƙasashen yankin da ke duba batun tsaro da muggan ƙwayoyi dama rikicin siyasar day a dauki lokaci yana barazana ga makomar Kasar Guinea Bissau da ta rasa shugabanta a cikin watan Janairun da ya gabata.
Rikicin kuma da ya dauki hankalin ita kanta majalisar dinkin duniya da babban wakilinta a yankin sa'eed jinnit yace a shirye take domin taimakawa kasashen na ecowas tunkarar kalubalen dake tada hankula a ciki da ma wajen yankin baki ɗayansa.
Game da annobar 'yan fashin jiragen ruwa, muna kawo shawarar bukatar Majalisar Ɗinkin Duniya na aiki tare da ECOWAS da ƙungiyar haɗa kan ƙasashen Afirka ta tsakiya da hukumar ruwayen Guinea wajen tara kuɗi da taimakawa kasashen da matsalar ta shafa na gudanar da wani taron da burin sa zai zamo gina sabuwar dabarar yaki day an fashin ta zamani.
To sai dai kuma duk da cewar majalisar ta taka rawa wajen neman hanyoyin tunkarar matsalolin tsaro da siyasar yankin daga dukkan alamu akwai kaffa kaffa a ɓangaren wasu daga cikin kasashen da wannan taimako ke iya yiwa rana.
Dr Nuruddeen Muhammed dai na zaman karamin ministan harkokin wajen tarrayar Nigeria daya kuma daga cikin kasashen dake kan gaba ga batun na rashin tsaro a ɗaukacin yanki.
Sharaɗi na agaji ko kuma siyasa irin ta son rai dai ana cigaba da musayar yawu dama kila nuna a tsakanin ƙasashen da yanzu haka suka sha bambam kan batutuwa da dama da suka hada da batun shugabanci dama uwa uba na tsaron al'ummar yanki.
Bazuum Mohammed dai na zaman ministan harkokin wajen jamhuriyar nigeriar daya kuma daga cikin kasashen da ke fuskantar barzanar yayan kungiyar Alqaida a yankin yammacin Africa.
To sai dai kuma ganin bayan alqaida da ma ragowar kawayen su dake yankin na ecowas ko kuma nuna yatsa a tsakanin juna dai , ana hasashen yiwuwar karuwa da ma tasirin irin wadannan kungiyoyin a cikin ECOWAS ɗin dake fama da mummunan talauci da kuma ake zargin shugabaninta da rashin iya mulki na gari.
To sai dai kuma a cewar Salamatu Sulaiman dake zaman kwamishinar kula da tsaro da zaman lafiya ta hukumar ecowas , kasashen kungiyar ba zasu karaya bag a kokarin fuskantar annobar da ta gagari turawan yamma masu takamar ƙarfi da ƙarfe.
Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Mohammad Nasiru Awal