TARON COMMONWEALTH A ABUJA
December 3, 2003Talla
Rahotan daya fito gabannin tarion shugabannin na kasashen Commonwealth dazai gudana a Abuja na nuni dacewa ba zaa iya cimma ingantacciyar democradiyya ba tare da an bawa mutane daman tofa albarkacin bakinsu ba,da kuma basu daman sanin me gwamnati ke ciki.
Rahotan mai suna open Sesame wadda wata kungiyar fafutukan kare hakkin biladama dake da zama a India ta rubuta,na kira ga shugabanni dasu gaggauta daukan matakan kafa dokoki da zasu bawa jamaa daman aiki tare da gwamnatocinsu.Bugu da kari ya zamanto wajibi wa kungiyar ta Commonwealth ta samar da wani yanayi na mahawara tsakanin jamaa dangane da tsare tsare na gwamnati.Idan ba haka akayi ba,babu yadda zaa cimma democradiyya da cigaban kasa.
Akasarin kasashen dake da wakilci a kungiyar basa bawa jamaa yancin su.11 daga cikin kasashje 54 dake kungiyar ne kadai suke da sukuni akan dokoki na yada labaru,ayayinda wasu ke rubuce a kundun tsarin mulkin kasashen amma baa amfani dasu.Ana nufin an koma mulkin mallaka a lokacin mulkin Britania?Daman dai Commonwealth kungiyar kasashe ce da Britania ta mulka,kuma bisa dukkan alamu haka yake. Rahotan yace hukumomin mulkin mallaka na amfani da sirri wajen nuna ikonsu daga nesa,wanda irin hakan ne ke kare jamaa daga sanin abunda gwamnati ke ciki.A dangane da hakane yawancin kasashe ayau ke cigaba da amfani da wannan tsari,kamar har yanzu ana karkashin mulkin mallaka ,domin babu alamun sauyi.
Ana yawaita samun matsaloli na ayyuka na sirri tsakanin jamiai,hana tsare masu laifi,dokokin yaki da taaddanci,da wasu dokoki da suka shafi yancin kafofin yada labaru.
A dangane da hakane wannan rahoto ke kira ga taron shugabannin na kungiyar Commowealth na wannan shekara ta 2003,dasu tabbatar dacewa yancin tofa albarkacin baki ko kuma sanin harkokin gwamnati shine kadai madogara wajen ingantaccen Democradiyya da cigaba.Kuma kungiyoyin kare hakkin biladama zasu zuba ido domin ganin yadda wakilan kungiyar zasu tabbatar da haka.Bugu da kari a tallafawa kasashe wakilai wajen aiwatar da wannan tsarin,kana kungiyar ta bude kofar halartan taron ministocin gudanarwanta,ayayinda yake da muhimmancin cikin kowace shekara biyu kasashe su gabatar da sakamakon nasara da suka cimma akan wannan batu akowane taro na shugabannin na Commonwealth.
A misalin data bayar kungiyar kare hakkin biladaman tace kasashe kamar India,Nigeria,Pakistan da Bangladash,masu yawan jamaa nan ne ake fuskantar ire iren wadannan matsaloli da jamaa basa sanin abunda gwamnati take ciki.A dangane da hakane ake gazawa wajen cimma nasara kann inganta wadannan kasashe,tunda akwai babban gibi tsakanin gwamnati da jamaar kasa.Domin talakawa sun san bukatunsu,amma babu daman furtawa domin gudun fushin gwamnati.

Talla