Afirka: Dakile kwararar bakin haure a Turai
May 13, 2025Wakilai sama da 100 ne daga kasashen Afirka da nahiyar Turan suka hallara a Abuja fadar gwamnatin Najeriya, a kokarin shawo kan matsalar ta kaurar da matasa ke yi daga nahiyar Afirka zuwa Turai ta haramtacciyar hanya. Taron da suka yi a karkashin kudurin Rabat da ya samar da dama ta aiki tare da nufin yi wa matsalar taron dangi, domin a zamanantar da ita. Kaso 30 na bakin da ke kaura daga Afirka zuwa Turan dai, dukkaninsu matasa ne da wadanda ke da kanana shekaru da ba su mallaki hankalinsu ba.
Daukacin kasashen Turai dai na aiki ne da hadin guiwar kasashen Afirka da kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO, domin dakile matasan da ke kauran wadanda kaso 20 cikin 100 ke bin hanyoyi da suka sabawa doka. Jamhuriyar Nijar dai ta zama wata hanya da masu kaura ta hanyar da ba ta dace ba daga yankin Afirka ta Yamma ke bi, domin zuwa nahiyar Turai. Najeriya dai na cikin kasashen da wannan matsala take da girman gaske, inda gwamnati ta bayyana daukar matakai na shawo kanta. Nahiyar Turai da Afirka na son ganin yadda za su zamanantar da tsarin kaurar da matasa ke yi ta hanyara koya masu ilimi da sana'oi, domin su iya kaura tare da ilimi da sana'a mai tsari da mutunci da kuma kima.