Taron ƙolin Amirka da Tarayyar Turai
November 29, 2011Amirka ta yi tayin tallafawa ƙungiyar tarayyar turai a dangane da matsalar bashi da ta dabaibaye ƙasashen ƙungiyar masu amfani da kuɗin bai ɗaya na euro. Sai dai kuma Washington ta ce ba za ta bada gudunmawar kuɗi domin ceto tattalin ƙasashen 17 masu amfani da kuɗin na euro ba. A jiya Litinin shugaban Amirka Barack Obama da sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton da sakataren kuɗin Amirkan Timothy Geithner suka yi ganawar sirri a fadar White House tare da shugaban majalisar Turai Herman Van Rompuy da shugaban hukumar tarayyar Turan Jose Manuel Barroso da kuma Kantomar harkokin wajen tarayyar Turai Catherine Ashton. Shugaba Obama yace makomar ƙasashen na turai masu amfani da kuɗin euro zai yi tasiri ga farfaɗowar tattalin arzikin Amirka. Sai dai kuma yayin aka sami rarrabuwar kawuna a tsakanin ƙasashen Turan kan yadda za'a shawo kan matsalar a waje guda shugaban hukumar tarayyar Turan Jose Manuel Barroso ya tabbatarwa da Amirka cewa ƙungiyar tarayyar Turan za ta samo mafita ga wannan matsala.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Zainab Mohammed Abubakar