Taron ƙasashen ƙungiyar Tarrayar Turai
January 31, 2012Talla
Ƙasashe guda 25 cikin 27 suka amince da yarjejeniyar wacce ta tanadi yi hukumci akan wata ƙasar da ta kauce wa yin amfani da tsarin na baiyana kasafin kudinta ga ƙungiyar.
Tare da samar da wani asusun ceto na dindin ga ƙasashen da ke fama da matsalar tattalin arziki irin su Girka da Portugal da kuma waɗanda zasu iya samun kan su cikin irin wannan hali a nan gaba:Sai dai ƙasashe biyu Britaniya da Tcheque basu yardda ba da yarjejeniyatr ba kuma shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy ya baiyana dalilai ''ya ce fraministan ƙasar Tcheque ya sanar da mu cewar akan wasu dalilai na kudin tsarin mulki kasar sa baza ta iya rataɓa hannu ba akan yarjejeniyar ba.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi